"Na Gano Mafita," Sarki Sanusi II Ya Shirya Kawo Karshen Rikicin Fulani a Najeriya

"Na Gano Mafita," Sarki Sanusi II Ya Shirya Kawo Karshen Rikicin Fulani a Najeriya

  • Muhammadu Sanusi II ya bayyana aniyarsa ta kawo mafita a rikicin Fulani matuƙar ya samu goyon bayan gwamnatin tarayya
  • Sarkin Kano na 16 ya ce an zalunci Fulani ta hanyoyi da dama wanda yake ganin lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen lamarin a yau
  • Basaraken ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wata kungiyar kabilar Fulani a fadarsa da ke birnin Kano ranar Talata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin Fulani da ke faruwa a kasar nan.

Sarkin ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar har abada, yana mai cewa hakan ba za ta faru ba sai da taimakon gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

“Hadama ba za ta barsu ba”: Kwankwaso kan hadakar Atiku da ’yan adawa a 2027

Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi ya ce zai iya warware rikicin Fulani a Najeriya Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Fulani sun ziyarci Sarki Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin kungiyar Fulani, 'Tapital Pulaku Njode Jam Nigeria' a fadarsa da ke Kano yau Talata, Punch ta tattaro labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Sanusi II ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta samar da mafita ta din-din-din game da rikicin Fulani makiyaya da ya addabi sassan ƙasar nan.

Yadda za a kawo karshen rikicin Fulani

A rahoton Leadership, Sarki Sanusi II ya ce:

"Hakan za ta yiwu ne idan gwamnatin tarayya ta ba ni goyon baya saboda tana da ƙarfi da duk abin da ake bukata da har dabaru na za su yi aiki.
An yi watsi da Fulani kuma ba haka ya kamata ba, lokaci ya yi da gwamnati za ta haɗa kai da mu wajen samar da mafita musamman rikicin Fulani da manoma."

Kara karanta wannan

"Rudewa suka yi," Bature ya yi martani kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu

"Ni a shirye nake na taimaka wa gwamnati ta cimma burinta na samar da zaman lafiya a tsakanin Fulani da sauran ’yan Najeriya, a daina cutar da su, ina da yaƙinin hakan zai yiwu."

Sarki Sanusi II ya kara da musanta ikirarin cewa akwai bara gurbi a cikin Fulani, waɗanda suka shafa masu kashin kaji har ake masu kuɗin goro.

Hadimin Tinubu ya magantu kan tallafin mai

A wani rahoton kuma fadar shugaban ƙasa ta sake nanata cewa tallafin fetur ya zama tarihi tun bayan kalaman Bola Tinubu a Mayun 2023.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka ranar Talata, 3 ga watan Satumba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262