Bayan Kammala Ziyara a Faransa, Jirgin Tinubu Na Shirin Lulawa Kasar Waje

Bayan Kammala Ziyara a Faransa, Jirgin Tinubu Na Shirin Lulawa Kasar Waje

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai sake lulawa zuwa ƙasar China domin halartar wasu muhimman tarurruka
  • Ziyarar da shugaban ƙasan zai kai zuwa ƙasar China na zuwa ne bayan ya kammala wata ziyara da yaje yi a ƙasar Faransa
  • Ziyarar wacce Shugaba Tinubu zai kai a China a cikin farkon watan Satumba, ita ce ziyararsa ta farko a ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin kai ziyarar aiki zuwa ƙasar China.

Shugaba Tinubu zai ziyarci ƙasar China ne bayan kammala ziyarar da yaje yi a ƙasar Faransa.

Tinubu zai je ziyara kasar China
Shugaba Tinubu zai ziyarci kasar China Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya sanar da kai ziyarar da Tinubu zai yi zuwa China a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa da ke Abuja a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: An samu matsala a taron da gwamnatin Tinubu za ta ya da ASUU

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Tinubu zai je China?

Da yake jawabi ga taron manema labarai, Ajuri Ngelale ya ce Tinubu zai halarci wani taro ne a ƙasar China wanda ake sa ran za a yi a cikin satin farko na watan Satumba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya bayyana cewa taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnati mai ci ke yi domin inganta rayuwar ƴan Najeriya.

A ƙasar China, ana sa ran Tinubu zai gana da shugaban ƙasar, Xi Jinping, inda za su rattaɓa hannu kan wasu yarjejeniyoyi.

Shugaba Tinubu zai kuma gana da shugabannin kamfanoni guda 10 a ƙasar da ke a ɓangarorin man fetur da gas, noma da sauransu.

Karanta wasu labaran kan Tinubu

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi lokacin da 'yan Najeriya za su samu sauki

Tinubu ya kwantar da hankalin ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na ɗaukar matakai masu tsauri da nufin kawo sauƙi ga ƴan Najeriya.

Shugaba Tinubu ya sha alwashin cewa nan ba da jimawa ba manufofinsa za su kawo sauki ga ƴan Najeriya kan halin matsin da suka tsinci kansu a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Tags: