Jami'an Tsaro Sun Tono Bama Bamai a Garuruwa da Dama a Arewacin Najeriya
- Jami'an tsaro sun tono abubuwan fashewa da bama-bamai a garuruwa daban daban a wasu sassan jihar Neja
- Mai magana yawun ƴan sanda, SP Wasiu Abiodun ya ce sun gano waɗannan miyagun makamai ne tsakanin 2021 zuwa 2023
- Ya ce tuni jami'an ƴan sanda na sashin kwance bama-bamai suka lalata su a ranar 22 ga watan Agusta, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Jami'an tsaro sun tono wasu abubuwan fashewa da bama-bamai a wurare daban-daban a wasu sassan jihar Neja.
Daga cikin wuraren da aka tono bama-baman har da Galadima-Kogo da ke ƙaramar hukumar Shiroro, Mutun-ɗaya a Mangu da unguwar Gbeganu a Minna.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Litinin, Daiy Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda jami'an tsaro suna tono bama-bamai
Ya ce jami'ai sun gano ababen fashewar ne a lokacin ayyukan yaki da ta'addanci tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023 a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.
A karamar hukumar Shiroro, musamman Galadima-Kogo tashin bam ya yi mummunar ɓarna a 2022, wanda ya yi sanadin asarar jami’an tsaro na NSCDC.
Rundunar hadin gwiwa ta ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ne suka gano wadannan bama-baman da aka boye aka binne su a wurare daban-daban a Neja.
Niger: Wane mataki daka ɗauka?
Mai magana da yawun ƴan sandan ya ƙara da cewa tuni ana lalata dukkan abubuwan fashewar da bama-baman da aka tono, Channels tv ta tattaro.
SP Wasiu Abiodun ya ce an lalata kayayyakin ne a ranar 22 ga watan Agusta, 2024, a wani wuri da ke bayan Zuma Rock, a Suleja.
Babban jami'im sashin kwance bama-bamai na rundunar ƴan sandan, SP Mohammed Mamun ne ya jagoranci lalata bama-baman in ji Abiodun.
Yan bindiga sun sace darakta a Ribas
A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun sace wani darakta da ke aiki a hukumar tattara kuɗaden shiga ta jihar Ribas, Sir Aribibia John Fubara.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wuta a iska kafin daga bisani su tasa abin harin su zuwa wurin da har yanzun ba a gano ba.
Asali: Legit.ng