Wasu Ƴan Arewa Sun Yi Allah Wadai da Kisan Sarkin Gobir, Sun Aika Saƙo ga Gwamnoni

Wasu Ƴan Arewa Sun Yi Allah Wadai da Kisan Sarkin Gobir, Sun Aika Saƙo ga Gwamnoni

  • Wasu ƴan Arewa sun nuna takaicisu kan yadda gwamnatin Sakkwato ta gaza kare rayuwar Sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa
  • Ƙungiyoyin RAID da NRM sun bukaci gwamnatin tarayya da gwamnonin Arewa su ƙara ɗaukar matakan dawo da zaman lafiya
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa tare da kashe hakimin Gatawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sokoto

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Wasu ƙungiyoyin ƴan Arewa biyu, RAID da NRM, sun yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir kuma hakimin Gatawa a jihar Sakkawato, Isa Muhammad Bawa.

Ƙungiyoyin sun yi kira ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu da ta bullo da sabbin dabarun kare rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: An samu matsala a taron da gwamnatin Tinubu za ta ya da ASUU

Sarkin Gobir.
Wasu kungiyoyin Arewa sun bukaci gwamnatin Tinubu da gwamnoni su kara ɗaukar matakai kan sha'anin tsaro Hoto
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa shugaban RAID, Kwamared Balarabe Rufa'i, shi ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya koka kan yadda yadda miyagu ke kashe rayukan mutane da sarakuna a Arewacin Najeriya, inda ya buƙaci gwamnati ta tashi tsaye.

RAID da NRM sun soki gwamnatin Sokoto

Kwamared Balarabe, a madadin kungiyoyin biyu, ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnatin jihar Sakkwato ta yi sakaci bayan an yi garkuwa da Sarkin Gobir.

Ya bukaci ministan tsaro, Badaru Abubakar; ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle da hafsoshin tsaro su rubanya kokarinsu wajen maido da zaman lafiya a Arewa.

A rahoton Guardian, Kwamared Balarabe ya ce:

"Mu a RAID da NCM da daukacin ƴan Arewacin Najeriya ba mu ji daɗin abin da gwamnatin jihar Sakkwato ta yi ba.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa ya maida martani bayan ɗan Sarkin Gobir ya faɗi wanda ya sa a kashe babansu

"A matsayin shugaban tsaro na jiha, gwamna ya gaza ceto rayuwar basaraken da ya shafe sama da shekaru 40 yana yiwa al'umma da jihar hudima."

Ƙungiyoyin sun aika sako ga gwamnoni

Balarabe Rufai ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su ƙara ɗaukar matakai domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Har ila yau shugaban kungiyoyin biyu ya buƙaci gwamnoni su ɗauki sha'anin tsaro a matsayin abin da za su fi ba fifiko a gwamnatocinsu.

"Muna kira ga gwamnonin yankin Arewa da su mayar da hankali kan rashin tsaro, su ɗauki lamarin tsaro matsayin babban abin da za su fi ba fifiko."

Ɗan majalisa ya ƙaryata hannu a sace Sarkin Gobir

A wani rahoton kuma ɗan majalisar dokokin Sakkwato mai wakiltar Sabon Birni, Aminu Boza ya musanta zargin hannu a garkuwa da marigayi Sarkin Gobir.

A wani faifan bidiyo, ɗan marigayi sarkin ya bayyana abin da ƴan bindiga suka faɗa masu kafin su kashe babansu, Isa Muhammad Bawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: