Ana Fama da Matsin Rayuwa, Gwamna a Arewa Ya Sayo Motocin Alfarma Sama da 10
- Domin inganta ayyukan shari'a, Gwamna Ahmed Ododo ya saya wa alƙalai sababbin motoci 11 a jihar Kogi
- Gwamnan ya yi alkawarin cewa zai kara sayawa alkalan ƙarin motoci domin su samu damar sauke nauyin da ke kansu cikin adalci
- Babban alƙalin jihar Kogi ya godewa gwamnan bisa cika alƙawarin da ya ɗauka na samar da motocin aiki ga akalai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, a ranar Talata, ya miƙawa alkalai karin motoci 11 da ya sayo masu domin sauƙaƙa aikinsu.
Gwamnan ya damƙawa babban alkalin jihar, Josiah Mejabi sababbin motocin a wani biki da aka shirya a filin Muhammad Buhari Square da ke Lokoja.
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa yayin miƙa sababbin motocin, Gwamna Ododo ya yi alƙawarin sayo ƙarin wasu domin rabawa alƙalai su samu saukin zuwa aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Gwamna Ododo ya sayo motocin?
"Wannan na cikin alƙawurran da na ɗaukarwa ma'aikatan shari'a a ranar da muka rantsar da sababbin alƙalai a watan Yuli, za mu sayo ƙarin motoci.
"A waccan ranar mun raba motoci 14 kuma a yau ga shi za mu ƙara ba da motoci 11 ga alƙalan mu masu jajircewa da aiki tuƙuru.
"Muna fatan za mu kara sayo wasu nan ba da daɗewa ba domin ba kowane alkali a faɗin jihar Kogi."
- Gwamna Ahmed Ododo.
Ahmed Ododo ya buƙaci alkalan su biya wannan karamci da gwammnati ta yi masu ta hanyar yin adalci ga duka mutanen da suna kawo masu ƙorafi a kotunan su.
Alƙalai sun godewa Gwamna Ododo
Da yake mayar da martani, babban alkalin ya gode wa gwamnan bisa cika alkawarin da ya yiwa bangaren shari’a na ba alkalai motocin aiki, Tribune Nigeria ta rahoto.
Alkalin ya ce motocin za su taimaka musu matuƙa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata domin tabbatar da adanci da zaman lafiya a tsakanin al'umma.
Gwamnatin Katsina ta cire dokar hana fita
A wani rahoton kuma muƙaddashin gwamnan Katsina, Farouk Lawal Jobe ya cire dokar hana fita da aka sanya a ƙananan hukumomin jihar.
Sakataren gwamnatin Katsina, Abdullahi Faskari ne ya bayyana hakan ranar Talata, ya ce mutane na da damar ci gaba da harkokinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng