Zanga Zanga: Sojoji Sun Ci Karo da Gomman Matasa a Cikin Mota, Sun Ɗauki Mataki
- Sojoji sun kama wata babbar motar dakon kaya ɗauke da mutane 32 a garin Mararaba da ke jihar Nasarawa ranar Jumu'a
- Wani mazaunin yankin, Adamu Yau ya ce motar ta kawo shanu ne a yayin komawa direban ya ɗauki wasu ƴan acaba da kayansu
- Dakarun sojojin Najeriya sun nuna ba su yarda da su ba saboda zanga-zangar da ake yi kan tsadar rayuwa a faɗin ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Jami'an sojojin da aka tura garin Mararaba a jihar Nasarawa domin su kwantar da tarzomar masu zanga-zanga sun tare wata mota maƙare da matasa.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin sun tare babbar motar dakon kaya ɗauke da mutane 32 a Mararaba yau Jumu'a, 9 ga watan Agusta, 2025.
Wani mazaunin garin Adamu Yau ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:40 na safiyar ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin ya ce tun farko direban babbar motar ya kawo shanu ne a kasuwar da ke garin kuma a hanyar komawa ya ɗauki wasu domin rage masu hanya.
Zanga-zanga: Wasu mutane ne a motar?
Adamu Ya'u ya ce daga cikin waɗanda direban ya kwasa har da ƴan acaba da baburansu da kayayyakin su.
"Wasu daga cikin fasinjojin sun fada mani cewa sun shiga motar ne domin zuwa garin Dei-Dei da ke babban birnin tarayya Abuja.
"Kuma sun zaɓi hawa motar ne don kauce wa jami’an kula da ababen hawa, wadanda suka saba kame babura a kan babbar hanyar zuwa Abuja," in ji shi.
Dalilin sojoji na kama motar
Adamu ya ƙara da cewa ga dukkan alamu dakarun sojojin sun damu da yawan waɗanda ke cikin motar ne saboda zanga-zangar da ake yi a ƙasar nan.
"Sojojin sun kama motar da karfe 8:00 na safe kuma sun umarci duka waɗanda ke ciki su sauko ƙasa, yanzu haka suna bincikarsu ɗaya bayan ɗaya."
Bayanai sun nuna sojojin na ci gaba da bincikar mutanen har zuwa ƙarfe 11:00 na safiya lokacin da aka tattara wannan rahoton, cewar Punch.
Gwamna Makinde ya musanta ikirarin Tinubu
A wani labarin kuma Gwamna Seyi Makinde ya musanta ikirarin Bola Ahmed Tinubu na rabawa jihohi N570bn domin ragewa al'umma raɗaɗin kuncin rayuwa.
Tun farko shugaban ƙasa ya ce gwamnatinsa ta rabawa gwamnoni maƙudan kuɗi domin su faɗaɗa shirye-shiryen tallafawa ƴan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng