'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane '30' a Mummunan Harin da Suka Kai Jihar Benue

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane '30' a Mummunan Harin da Suka Kai Jihar Benue

  • Ƴan bindiga sun kashe akalla mutane 30 a kauyen Ayati, ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa da yiwuwar waɗanda aka kashe a harin su haura 50 saboda har yanzun ana kan binciken gawarwaki yau Jumu'a
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene ta tabbatar da harin wanda ƴan bindiga suka kai a daren jiya Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Akalla mutane 30 ne rahotanni suka tabbatar wasu ‘yan bindiga sun kashe a kauyen Ayati da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benuwai.

Wannan kashe-kashen na zuwa ne wata guda bayan mahara sun kashe wasu mazauna kauyen 11 wanda ya haifar da zanga-zanga a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Kaico: Ƴan bindiga sun hallaka basarake, sun yi awon gaba da mata da ƙananan yara

Yan sandan Najeriya.
Yan bindiga sun kashe mutane '30' a sabon harin da suka kai jihar Benue Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Mazauna yankin sun ce sabon harin da ya yi ajalin mutane 30 ya faru ne ranar Alhamis (Jiya) a Ayati, hedkwatar gundumar Borikyo, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Benue: Ana fargabar mutane 50 aka kashe

Wani mazaunin garin ya shaida wa wakilin jaridar ta wayar tarho cewa mutanen da aka kashe za su iya haura 50.

Ya ce har zuwa safiyar yau Juma'a, mutane na ci gaba da ƙoƙarin zaƙulo gawarwakin waɗanda aka kashe a cikin jejin da ke kusa da Ayati.

Cif Ayati Shima, wani fitaccen dan siyasa ɗan asalin garin, ya ɗora alhakin asarar rayukan kan gazawar shugabannin siyasa wajen dakile matsalar tsaro a yankin.

Shima, wanda tsohon dan takarar gwamna ne, ya ce an gano gawarwaki sama da 30 a yayin da masu aikin ceto ke cigaba da tsefe daji domin gano sauran mutanen da suka bata.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Sojoji cun ci karo da gomman matasa a cikin mota, sun ɗauki mataki

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamari, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

"Na samu labarin cewa an kai harin kuma a halin yanzu ina jiran ƙarin bayani daga jami'an ƴan sandan yankin," in ji Anene.

Yan bindiga sun kashe mutum 6

A wani rahoton kuma yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe mutane shida a kauyuka huɗu da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna.

Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane 26 a hare-hare daban-daban da suka kai a kauyukan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: