Shugaba Tinubu Ya Naɗa Tsohon Gwamnan Katsina a Shirgegen Muƙami, Ya Tura Saƙo
- Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban gudanarwan TETFund
- Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya sanar da haka ranar Talata, ya ce an naɗa mambobi 6 a hukumar tarayyar
- Tinubu ya buƙaci sababbin mambobin hukumar da su maida hankali wajen sauke nauyin da ke kan TETFund na tallafawa makarantu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, a matsayin sabon shugaban majalisar gudanarwa ta TETFund.
Aminu Bello Masari, tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya ya yi gwamnan Katsina na tsawon shekaru takwas daga 2015 zuwa 2023.
Aminu Masari ya samu kujera a TETFund
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna mai ci, Malam Dikko Umaru Radda shi ne ya gaji Masari a Katsina bayan samun nasara a zaben gwamnan da aka yi a watan Maris, 2023.
Bola Tinubu ya yi naɗi a TETFund
Mista Ngelale ya ƙara da cewa shugaban ƙasar ya kuma naɗa wasu mutum shida a matsayin mambobin majalisar gudanarwa ta asusun kula da manyan makarantu TETFund.
Sun hada da Sanata Sani Danladi, Sunday Adepoju, Nurudeen Adeyemi, Esther Onyinyechukwu Ukachukwu, Turaki Ibrahim da kuma Aboh Eduyok.
Shugaba Tinubu ya buƙaci sababbin mambobin gudanarwa na TETFund da su yi amfani da ƙwarewarsu wajen inganta manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya tura masu saƙo
"Shugaban ƙasa na fatan sababbin mambobin gudanarwa a wannan hukuma mai girma za su maida hankali wajen aiwatar da manufar TETFund.
"Yana fatan za su samar da tallafin da ake buƙata a manyan makarantu domin inganta harkokin ilimi," in ji Ngelale.
An janye zanga-zanga a Osun
A wani rahoton kun ji cewa masu zanga zanga sun dakatar da ita saboda matsowar bikin al'adun Osun-Osogbo na wannan shekarar 2024 a jihar Osun.
Matasan sun mika takardar bukatursu ga mataimakin gwamna kuma an yi masu alkawarin cewa za ta isa ofishin shugaban ƙasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng