Jerin Ƙasashe 4 da Zanga Zanga Ta Kawo Sauyin Gwamnati a Nahiyar Afirka

Jerin Ƙasashe 4 da Zanga Zanga Ta Kawo Sauyin Gwamnati a Nahiyar Afirka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024 ƴan Najeriya suka fara zanga-zangar adawa da halin kunci da manufofin gwamnati suka jefa ƙasar a ciki.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi iya bakin kokarinsa wajen daƙile zanga-zangar amma matasa suka kafe kan cewa babu fashi sai sun fito sun nuna damuwarsu.

Masu zanga zanga.
Kasashen da zanga-zanga ta kawo sauyi a gwamnati a nahiyar Afirka Hoto: Khalipha Umar
Asali: Facebook

Zanga-zangar lumana a Najeriya

Duk da kiraye-kirayen malamai da sarakuna da sauran masu faɗa a ji, masu shirya zanga-zangar waɗanda galibi matasa ne sun fito kan tituna ranar Alhamis da ta wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta haɗa muku jerin ƙasashen da zanga-zanga kan wani abu ya jawo sauyin gwamnati a nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

Jerin jagororin zanga zanga da jami'an hukumar DSS suka cafke

1. Sudan a 2019

A ƙasar Sudan, zanga-zangar ta ɓarke ne a watan Disambar 2018 saboda hauhawar farashin kayayyakin masarufi kamar burodi da man fetur da sauran su.

Zanga-zangar ta kara karfi a fadin kasar Sudan kuma zuwa watan Afrilun 2019, masu zanga-zangar suka fara yunkurin hamɓarar gwamnati.

Rahoton BBC ya tattaro cewa wannan zanga-zanga ce ta kawo ƙarshen mulkin shugaba Omar Al-Bashir, wanda ya shafe shekaru 30 yana mulkin ƙasar.

An kifar da gwamnatin Bashir ne tare da goyon bayan sojoji, waɗanda suka karbi mulkin, to amma masu zanga-zanga sun ci gaba da fafutukar kafa gwamnatin farar hula.

Wannan ya sa aka kafa majalisar mulkin Sudan, wadda ta hada da ‘yan zanga zanga da mambobin kwamitin rikon kwarya na soja. 

2. Burkina Faso a 2014

Wikipedia ta ce a watan Oktoba, 2024 jerin zanga-zanga da tashe-tashen hankula suka ɓarke a Burkina Faso kan yunkurin shugaban ƙasa Blaise Compaoré na neman tazarce.

Kara karanta wannan

Matasa sun yanke shawara, sun dakatar da zanga zanga saboda babban bikin al'ada

Zanga zangar ta yaɗu zuwa birane da dama cikin ƙanƙanin lokaci kuma an fara ta ne a matsayin martani ga yunƙurin canza kundin tsarin mulki don ba shugaban tazarce bayan shekaru 27 a mulki.

Matasa da kungiyoyin fararen hula ne suka jagoranci zanga-zangar, wadda ta kai ga ƙona zauren majalisar dokoki da wasu kadarorin gwamnati da ƙona hedkwatar jam'iyya mai mulki.

Daga karshe Shugaba Compaoré ya rusa gwamnati tare da ayyana dokar ta-baci kafin daga bisani ya tsere zuwa Cote d'Ivoire tare da goyon bayan shugaban na Ivory Coast, Alassane Ouattara.

3. Libya a 2011

Zanga-zangar da ta ɓarke kan adawa da mulkin Muhammad Qaddafi ta rikiɗe ta zama ta ƴan tawaye da makami a tsakiyar watan Fabrairu, 2011, rahoton Aljazeera.

A lokacin da ake dab da kawar da ƴan tawayen a watan Maris, sojojin kasa da kasa karkashin jagorancin NATO suka kaddamar da hare-hare ta sama kan dakarun Gaddafi. 

Kara karanta wannan

Rana ta 5: Zanga zanga ta ɗauki sabon salo, wasu matasa sun yi tsirara a kan titi

Duk da zuwan sojojin NATO ya ba ƴan tawaye nasara mai yawa amma Shugaba Qaddafi ya ci gaba da zama kan mulki a babban birnin kasar Tripoli.

A watan Agustan 2011 ne aka tilasta masa sauka daga mulki bayan da dakarun 'yan tawaye suka karbe iko da birnin Tripoli.

4. Tunusia a 2011

Ƴan ƙasar Tunusiya sun yi zanga-zangar nuna adawa da cin hanci da rashawa, talauci da danniyar siyasa wanda a karshe suka tilastawa shugaban ƙasa, Zine al-Abidine Ben Ali ya yi murabus.

Shugaban ya sauka ne a watan Janairu, 2011 bayan matsin lamba daga masu zanga zangar waɗanda suka ci gaba da yin arangama da jami'an tsaro.

Wannan lamari da ya shahara a kafafen yada labarai a matsayin "Juyin juya halin Jasmine," ya haifar da zanga-zangar irin wannan a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.

Gwamnatin Tinubu ta ja kunnen kasashen waje

A wani labarin kuma gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ko kaɗan ba za ta lamunce wasu ƙasashen waje su yi mata katsalandan a harkokinta na cikin gida ba

Kara karanta wannan

Rana Ta 3: Masu zanga zanga sun yi takansu yayin da jami'an tsaro suka buɗe wuta

Ministan harkokin ƙasashen waje wanda ya bayyana hakan ya yi barazanar gwamnatim za ta ɗauki mataki kan duk ƙasar da ta samu da laifi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262