Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Masu Zanga Zanga, Ta Umarci Su Ci Gaba da Zama a Wurare 2
- Babbar kotun jihar Legas ta ƙara yanke hukunci kan wuraren da ta amince matasa su yi zanga-zanga
- Mai shari'a ta tsawaita umarnin cewa ba ta yarda a yi zanga zanga a ko ina ba sai wurare biyu watau Preedom Park da Peace Park
- Ta ɗauki wannan matakin ne bayan kwamishinan shari'a na Legas ya bukaci tsawaita umarnin taƙaita wuraren zanga-zangar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Babbar kotun jihar Legas mai zama a Igbosere ta ƙara yanke hukunci kan wuraren da ya halatta matasa su yi zanga-zangar da suka fara a jihar.
Kotun ta tsawaita wa'adin umarnin da ta bayar a baya na taƙaita zanga-zangar matasan a wurare biyu, filin shaƙatawa na Freedom da filin shakatawa na Peace.
Mai shari'a S.I. Sonaike ce ta yanke wannan hukuncin a buƙatar da Antoni Janar kuma kwmaishinan shari'a na Legas, Lawal Pedro, SAN, ya shigar ta neman tsawaita umarnin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Legas ta nemi tsawaita dokar
Kamar yadda Leadership ta ruwaito, daraktan sashin shari'a, Hameed Oyenuga, shi ne ya wakilci kwamishinan shari'a na jihar Legas a zaman kotu yau Talata.
Ya shaidawa alkalin kotun cewa tuni aka kai takardar sammacin karar ga duka waɗanda ake ƙara a shari'ar watau wakilan masu zanga zanga.
A cewarsa, duk da cewa wadanda ake kara ba su amsa ba har yanzu, amma akwai bukatar a tsawaita dokar taƙaita zanga-zangar zuwa wurare biyu.
Wane hukunci kotu ta yanke a Legas?
Da take yanke hukuncu, mai shari'a Sonaike ta bayyana gamsuwarta bisa yadda Antoni Janar ya bi umarnin da mai shari'a Ogundare ya bayar tun farko, Channels tv ta rahoto.
Sannan ta ba da umarnin a takaita zanga-zangar a wuraren shakatawa na Fredom da na Peace da ke a yankunan Ojota da Ketu na jihar har sai an cika umarnin farko.
Masu zanga-zanga sun ɗauki hutu
A wani rahoton kuma jagororin da suka shirya zanga-zanga a jihar Legas sun sanar da janyewa domin duba ci gaba da suka samu tun da aka fara zuwa yau.
Kwamared Hassan Taiwo Soweto, ɗaya daga cikin jagororin zanga-zanga ya ce ba za su ji tsoron barazanar hukumomin tsaro ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng