Zanga Zanga: An Kama Mutumin da Ke Ɗinka Tutocin Ƙasar Rasha a Jihar Kano
- Jami'an tsaro sun kama wani tela mai suna Ahmed bisa zarginsa da yaɗa tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano a lokacin zanga-zanga
- Rahotanni sun nuna matasa sun fara ɗaga tutocin ƙasar ketaren ne a makon da ya wuce, amma lamarin ya ƙara ƙamari a ranar Litinin
- Shugaba Bola Tinubu dai ya gargaɗi masu zanga-zanga su dakata haka nan domin ba zai bari su ci ga a da tayar da yamutsi a kasa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa an damƙe daya daga cikin mutanen da ke dinƙa tutocin kasar Rasha a birnin Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
An tattaro cewa dubannin ƴan Najeriya da suka fita zanga-zangar kin jinin manufofin gwamnati mai ci sun fara ɗaga tutar ƙasar Rasha a jihohi daban-daban.
Daily Trust ta ce lamarin dai ya faru ne a makon da ya gabata a wurare ƙalilan, amma zuwa yau Litinin adadin wadanda ke daga tutoci ya karu sosai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya gargaɗi masu zanga-zanga
Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gargadi masu zanga-zangar da kada su bari a yi amfani da su wajen yada wata manufa da ta sabawa doka.
Shugaba Tinubu ya ce:
"Yanzu da muka shafe shekaru 25 muna shan romon mulkin dimokuradiyya, kada ku bari makiya su yi amfani da ku wajen tallata manufar da ta saɓawa tsarin ƙasarmu, da za ta mayar da mu baya."
Tutar Rasha: An kama tela a Kano
Sai dai a yau Litinin, dakarun ƴan sanda suka cafke wani tela da ke ɗinka tutocin rasha tare da wasu matasa da ke ɗaga tutocin a wurin zanga-zanga.
Bayanai sun nuna cewa an kama telan mai suna Ahmed Bello ɗauke da wasu tutocin ƙasar Rasha da yawa a hannunsa a Kano.
Tuni dai ƴan sanda suka sakaya shi a bayan kanta domin ci gaba da bincike kan lamarin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da hafsoshin tsaro a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja ana tsaka da zanga-zanga.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila sun halarci taron yau Litinin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng