Sarki Sanusi Ya Bayyana Mummunar Illar da Zanga Zanga Ta Jawo a Kano da Arewa
- Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayyana illar da zanga-zanga ta haifar a jihar da Arewacin Najeriya
- Sanusi II ya ce tun farko wannan tashin-tashinar malamai da shugabanni su ke gudu shiyasa suka yi ta kashedin a gujewa zanga-zangar
- Basaraken ya ce babu inda wannan zanga-zanga ta maida baya fiye da jihar Kano da Arewa, inda ya ƙara da cewa an yi asara da yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya ce an yiwa jihar Kano babbar illa a zanga-zangar da matasa suka yi ranar Alhamis.
Sarkin ya yi Allah wadai da rikicin da ya barke a jihar a ranar Alhamis duk da rokon da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na gudanar da zanga-zangar lumana.
Sanusi II wanda aka dawo da shi kan sarauta ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa da ke Kofar Kudu, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi II ya koka kan asarar rayuka
Da yake nuna takaicinsa kan tashe-tashen hankula da suka haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, Sanusi ya bayyana lamarin a matsayin wani babban koma baya ga jihar Kano.
"Abin da ya faru jiya shi ne abin da malamai da shugabanni suka yi ta gargadi na yiwuwar miyagu su shiga zanga-zangar, su yi amfani da ita wajen tada tarzoma wanda ya kai ga asarar rayuka, dukiyoyi da jikkata mutane.
“Kamar yadda muka fada a taron masu ruwa da tsaki, duk wani tashin hankali kan mu yake karewa. Matasan da suka mutu ‘ya’yanmu ne, dukiyoyin da aka kona ko aka sace na mutanen Kano ne.
"Mun maida kan mu baya, babu inda wannan zanga-zangar ta yiwa illa kamar Kano da Arewacin Najeriya,"
- Muhammadu Sanusi II.
Kano ta gamu da babban koma baya
Sanusi ya ce ya yi magana da minista kan za a zo buɗe sabuwar cibiyar fasahar zamani da aka gina amma masu zanga-zanga sun fasa wurin sun sace kwamfutoci.
Basaraken ya yi kira ga masu zanga-zangar da su hakura sun janye kuma kada su bari a yaudare su, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Yan sanda sun kama ɓarayi a Kano
A wani rahoton kuma rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana karin nasara a kan bata-garin da suka saci kayan jama'a yayin zanga-zanga a ranar farko.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kamen bayan jami'an tsaro sun ci gaba da aikinsu.
Asali: Legit.ng