Zanga Zanga: 'Yan Sanda na Kokarin Kakkabe Miyagu, An Kama 'Yan Daba 50 a Katsina

Zanga Zanga: 'Yan Sanda na Kokarin Kakkabe Miyagu, An Kama 'Yan Daba 50 a Katsina

  • Yayin da 'yan daba da sauran bata-gari su ka shiga cikin zanga-zanga tare da haddasa rikici, 'yan sanda sun dage da aiki
  • Yanzu haka rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke wasu 'yan daba guda 50 da ta gano su na daga cikin masu tayar da zaune tsaye
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan ya shaidawa manema labarai cewa duk da aikin miyagun, ba a samu asarar rai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Rundunar 'yan sandan Katsina ta bayyana matsayarta na tabbatar da kakkabe 'yan daba daga cikin masu gudanar da zanga-zanga a jihar.

Kara karanta wannan

Jama'a sun yi kunnen ƙashi, an fito zanga zanga a rana ta 2 duk da dokar hana fita

Talakawan Najeriya sun tsunduma zanga-zangar lumana ta kwanki 10, amma an samu wasu bata-gari da su ka yi amfani da damar wajen tayar da hankula.

Anadolu
An kama 'yan daba 50 a Katsina yayin zanga-zanga Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Katsina, ASP Abubakar Aliyu ya ce zuwa yanzu sun damke 'yan daba guda 50.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu asarar rai lokacin zanga-zanga," ASP Aliyu

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa yayin gudanar da zanga-zanga a jihar, sabanin wasu jihohin Arewacin kasar nan.

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa an samu wasu bata-garin matasa sun farfasa kayan gwamnati da kwashe kadarori ciki har da kayan wuta mai amfani da hasken rana.

Tuni gwamnatin jihar ta sanya dokar ta baci domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a tare da hana bata gari ci gaba da shigar rigar zanga-zanga suna sata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Yobe ta tsugunar da mutane 2,390, Boko Haram sun fatattaki jama'a

Masu zanga-zanga sun kona ofishin APC

A baya kun ji labarin yadda wasu matasa su ka cinnawa ofishin jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu ta APC wuta a jihar Kaduna yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a sassan kasar nan.

A jiya Alhamis ne aka fara zanga-zangar lumana ta kwanaki 10, amma ta rikide a wasu jihohin, mafi akasarinsu wadanda ke Arewacin kasar nan, inda aka samu rasa rayuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Tags: