'Yan Sanda Sun Buɗe Wuta Yayin da Masu Zanga Zanga Suka Toshe Babban Titi a Arewa

'Yan Sanda Sun Buɗe Wuta Yayin da Masu Zanga Zanga Suka Toshe Babban Titi a Arewa

  • Jami'an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a lokacin da suka yi yunkurin toshe babban titi a Minna, babban birnin jihar Neja
  • An dai jiyo karar harbe-harben bindiga da matasan suka matsa sai sun toshe titin bayan sun fara zanga-zanga yau Alhamis
  • Tuni dai aka ƙara girke jami'an tsaro a wurare masu muhimmanci waɗanda ake tunanin za a iya samun matsala a Minna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Ƴan sanda sun yi ta harbe-harbe a saman iska a babbar mahadar titin Top Medical da ke unguwar Tunga a Minna, babban birnin jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a lokacin da masu zanga-zanga suka yi yunƙurin toshe babban titin yau Alhamis, 1 ga watan Augusta, 2024.

Kara karanta wannan

Kano: ’Yan sanda sun tashi tsaye, matasa sun farmaki shaguna daga fara zanga zanga

Matasa da yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun yi harbe-harbe a sa'ilin da masu zanga zanga suka yi yunkurin toshe titi a Minna Hoto: @Naija_PR, @Nigerianstories
Asali: Twitter

Me ya kawo harbe-harbe a Neja?

Tun da farko dai ‘yan sandan sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar amma suka sake haɗuwa da nufin ɗora duwatsu a titin mai tara cunkoso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ganin haka ne ya sa ƴan sanda sakin wuta a saman iska domin tsorata masu zanga-zangar su bar wurin.

Tuni dai ‘yan sanda da ‘yan banga suka kwashe duwatsun da masu zanga-zangar suka yi amfani da su wajen tare wani bangare na titin.

An girke 'yan sanda da jami'an tsaro

Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, sojoji, jami'an shige da fice, jami’an tsaron fararen hula NSCDC sun mamaye wuraren da ake tunanin zanga zanga za ta yi zafi a Neja.

Daga cikin wuraren da aka girke jami'an tsaron har da babban shataletalen Kpakungu wanda ke kan titin Minna zuwa Bida.

Kara karanta wannan

Ana fargabar miyagu za su shiga zanga zanga, an samu hanyoyi 5 domin kare kai

Rahoton The Nation ya nuna cewa an rufe shaguna da kasuwanni a Minna domin gujewa abin da ka iya zuwa ya dawo na sace-sace a lokacin zanga-zanga.

Zanga-zanga: An fara yunƙurin fasa shaguna

Ku na da labarin an fara samun matsala a Kano yayin zanga-zanga bayan wasu matasa sun yi yunkurin fasa shaguna a birnin.

An tabbatar da cewa matasan sun kai farmakin ne a 'Zoo Road' da ke birnin Kano inda suka fasa wasu tagogi yayin zanga-zangar da aka fara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: