Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu a Dokar Sabon Mafi Karancin Albashi, Bayanai Sun Fito
- Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu a dokar sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000 a fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Litinin
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke faɗi tashin yadda za ta daƙile zanga-zangar da matasa suka shirya yi a Agusta
- Shugabannin majalisar tarayya karkashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio sun halarci taron FEC inda suka shaida sa hannun Shugaba Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya yau Litinin, 29 ga watan Yuli.
Wannan ya kawo ƙarshen dogon lokacin da aka shafe ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da ƙungioyin ƴan kwadago.
Sabon mafi karancin albashi ya zama doka
Channels tv ta tattaro cewa Bola Tinubu ya sa hannu kan kudirin dokar a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ranar Talata, 23 ga watan Yuli, 2024 majalisar tarayya ta amince da kudirin sabon mafi karancin albashi na N70,000 bayan shugaban ƙasar ya gabatar.
Ƴan majalisa sun shaida sa hannun Tinubu
Shugaban ƙasa ya sa hannu kan dokar a gaban wakilan majalisar tarayya karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu ƴan majalisar wakilai.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Bola Tinubu ya sa hannu a kudirin ne a taron majalisar zartaswa (FEC) wanda ke gudana yanzu haka a Aso Villa da ke Abuja.
FEC: Tinubu ya yi taro da 'yan majalisa
Wannan ne karo na farko tun bayan dawowar mulkin demokuraɗiyya da majalisar zartaswa ta amince ƴan majalisa suka shiga taron FEC.
Wakilan majalisar tarayya sun isa fadar shugaban ƙasa da misalin 1:38 na tsakar ranar yau Litinin.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar zanga-zangar da wasu ‘yan Najeriya ke shirin yi domin nuna adawa da tsadar rayuwar da ake fama da ita.
Zanga-zanga: Sojoji sun ɗauki mataki a Abuja
Ku na da labarin dakarun sojojin Najeriya sun mamaye babban titin Abuja zuwa Keffi kwanaki uku gabannin zanga-zangar da ake shirin yi.
A ƴan makonnin da suka shige, batun zanga-zangar da matasa ke shirin yi kan tsadar rayuwa ne ya fi jan hankali a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng