Tinubu: Wasu Bayanai Sun Fito Bayan Majalisa Ta Amince da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi
- Majalisar tarayya ta bayyana inda aka kwana kan batun sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000 wanda ta amince da shi
- Sanatoci da ƴan majalisar wakilai sun amince da kudirin albashin ranar Talata, 23 ga watan Yuli bayan shugaban ƙasa ya aiko da shi
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin majalisa, Abdullahi Gumel ya ce Bola Tinubu ka iya rattaba hannu kan kudirin a mako mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Bayanai sun nuna idan har komai ya tafi yadda aka tsara, Bola Ahmed Tinubu zai rattaɓa hannu kan kudirin dokar sabon mafi ƙarancin albashi a makon gobe.
Hakan na zuwa ne bayan majalisar dattawa da majalisar wakilai sun amince da kudirin ranar Talata, 23 ga watan Yuli, 2024.
Majalisar tarayya ta gama aikinta
The Nation ta tattaro cewa bayan amincewa da kudirin sabon mafi ƙarancin albashin N70,000, ana ci gaba da dakon lokacin da shugaban ƙasa zai rattaɓa hannu a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon albashi mafi karanci ga majalisa a ranar Talata, kuma ba tare da bata lokaci ba majalisun biyu suka amince da shi a ranar.
Jaridar Punch ta wallafa rahoto ranar Jumu'a, 26 ga watan Yuli cewa majalisa ta kammala komai da ya shafi kudirin ranar Laraba, 24 ga watan Yulin 2024.
Majiyoyi da dama daga zauren majalisa sun tabbatar da cewa bayan haka an tura kudirin ga shugaban ƙasa washe gari ranar Alhamis, 25 ga Yuli domin ya sa hannu.
Yaushe Bola Tinubu zai sa hannu?
Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin majalisa, Sanata Abdullahi Gumel, ya tabbatar da hakan a wata gajeruwar sanarwa da ya fitar jiya.
"Yau (Alhamis) za a miƙa kudirin (ga shugaban ƙasa)," in ji shi.
A halin yanzu dai ana jiran Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓa hannu kan kudurin ya zama doka domin fara aiwatar da shi.
Ma'aikata na ganin ba nan matsalar take ba
Wani ma'aikacin tarayya ɗan asalin jihar Katsina, Ibrahim Abdullahi ya ce sa hannu ba shi ne matsalar ba, sun fi so su ga an aiwatar.
Ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa duba da yadda aka saba a baya, zai wahala gwamnati ta aiwatar da sabon albashin a cikin wannan shekarar.
Ibrahim ya ce:
"Ni ina ganin ba a nan gizon ke saka ba, shugaban ƙasa zai iya sa hannu a ɗauki dogon lokaci ba tare da an aiwatar ba, muna fatan wannan gwamnati ta yi a kan lokaci."
Tinubu ya tono masu ɗaukar nauyin zanga-zanga
A wani labarin kun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙara yin tsokaci kan masu ɗaukar nauyin zanga-zanga da ake shirin yi a watan da ke tafe
Bola Tinubu ya bayyana cewa masu ɗaukar nauyin ba mazauna ba ne kuma suna shirya komai tare da tunzura mutane daga ƙasashen ketare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng