Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Yayin da Ginin Katafaren Otal Ya Rufta a Abuja

Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Yayin da Ginin Katafaren Otal Ya Rufta a Abuja

  • Mutane sun shiga fargaba a babban birnin tarayya Abuja a lokacin da wani ginin bene mai hawa huɗu ya ruguje ranar Litinin
  • Rahotanni sun nuna cewa ginin wanda ke da alaƙa da Otal ɗin Westbrook ya rufta kuma da yiwuwar ya danne mutane da dama
  • Tuni dai faifan bidiyon ruftawar benen ya bazu a kafafen sada zumunta yayin da jami'ai ke ci gaba da ƙoƙarin ceto a wurin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - An shiga damuwa da fargaba a lokacin da wani ginin bene na Westbrook Hotel ya rushe a yankin Garki da ke birnin tarayya Abuja.

Yanzu haka da muke haɗa wannan rahoton, ana fargabar ginin ya danne mutane da dama yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Kara karanta wannan

Kishin ƙishin din kara kudin fetur ya jawo kulle gidajen mai, jama'a sun shiga tasko

Ginin otal a Abuja.
Wani ginin Otal mai hawa huɗu ya ruguje a babban birnin tarayya Abuja Hoto: @Mobilepunch
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, an ce katafaren otal ɗin Westbrook na wani tsohon gwamna a jihohin Kudu maso Gabas ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abuja: Ana fargabar mutane sun mutu a otel

Wani ganau, wanda ya zanta da jaridar Punch bisa sharadin sakaya bayanansa ya ce akwai yiwuwar wasu sun mutu sakamakon rugujewar ginin ranar Litinin.

Ya ce a kan idonsa aka ciro wasu mutum biyu daga ɓaraguzan ginin kuma tuni aka wuce da su zuwa asibiti.

"Akwai yiwuwar mutanen da ginin ya rufta kansu sun mutu, na ga an ciro mutum biyu kuma an wuce da su zuwa asibiti yayin da ake ci gaba da lalube a wurin.
"Har yanzun jami'an bada agajin gaggawa ba su zo ba ballantana aikin lalubo mutane ya kankama a ɓaraguzan ginin."

Martanin ƴan Najeriya kan ruftawar ginin

Kara karanta wannan

An samu karin mutanen da suka mutu a harin bam da aka kai jihar Borno

Ƴan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da ruftawar ginin a soshiyal midiya. Legit Hausa ta tattaro muku wasu daga ciki.

@Simply_Tessy ya ce:

"Da yiwuwar wata ƴar sharholiya ta jawo mijin wata zuwa cikin ginin nan da ya rufta.

@Prinechoke ya ce:

"Kalli ɓaraguzan ginin da hukumomi suka amince da shi kuma ake kula da yadda ake tafiyar da ginin.

@CryptoSheffy102 ya ce:

"Idan kuka duba ɓaraguzan ginin cikin natsuwa zaku gane an yi amfani da kayan aiki mara inganci."

Gobara ta tashi a kasuwar Abuja

A wani rahoton kun ji cewa a yammacin ranar Alhamis, 27 ga watan Yunin 2024 ne gobara ta tashi a babbar kasuwar Karu da ke babban birnin tarayya Abuja.

An ruwaito cewa gobarar ta kama gadan-gadan yayin da jami'an hukumar kwana-kwana ke iya bakin kokarinsu domin shawo kanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel