Ministoci 3 da Manyan Jiga Jigai Sun Shiga Taron Kwamitin Mafi ƙarancin Albashi a Abuja

Ministoci 3 da Manyan Jiga Jigai Sun Shiga Taron Kwamitin Mafi ƙarancin Albashi a Abuja

  • Gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi yanzu haka a birnin tarayya Abuja
  • Ministan kudi, Wale Edun, ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, Atiku Bagudu da gwamnan Imo na cikin waɗanda suka halarci taron
  • Ana sa ran a wannan zama na yau Jumu'a ne kwamitin zai fito da sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan sabon mafi ƙarancin albashi ya shiga taro yanzu haka a birnin tarayya Abuja.

Taron yau Jumu'a, 7 ga watan Yuni, wanda shi ne karo na biyar tun bayan janye yajin aikin ƴan kwadago, yana gudana ne a Otal din Nicon Luxury Hotel.

Kara karanta wannan

NLC: Minista ya yi magana kan sabon mafi ƙarancin albashi bayan ya gana da Bola Tinubu

Kwamitin mafi karancin albashi ya shiga taro a Abuja.
Wakilan gwsmnatin tarayya, gwamnoni da ƴan kwadago sun sa labule a Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Manyan ƙusoshin gwamnati da sauran 'yan kwamitin sun halarci wannan zama da ake tsammani za a gama da batun sabon mafi karancin albashi, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kusoshin gwamnati a taron karin albashi

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Darakta-Janar na ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) da ƙaramar ministar kwadago da samar da ayyuka, Nkiruka Onyejeocha.

Sauran sun haɗa da ministan kuɗi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu da wakilan hukumar albashi da kuɗin shiga ta ƙasa.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma yana cikin waɗanda aka hanga sun shiga taron wanda ke gudana cikin sirri.

NLC na jiran sakamakon zaman yau

A taron da aka gudanar jiya Alhamis, mambobin kwamitin sun bayar da tabbacin cewa ƴan Najeriya ka iya sanin sabon mafi ƙarancin albashi bayan taron ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

"Karya ne," Gwamnati ta yi magana kan amincewa da biyan albashin akalla N105, 000

Idan ba ku manta ba ƙungiyoyin kwadagon sun dakatar da aikin da suka fara na tsawon mako guda, domin baiwa kwamitin damar kammala tattaunawa.

Haka nan NLC na fatan kwamitin zai zo da adadin sabon albashin wanda za a tura ga majalisar tarayya domin ta amince da shi sannan ya zama doka inji rahoton Daily Post.

Karin albashi: Tinubu ya gana da ministoci

A wani rahoton kuma, an ji Bola Ahmed Tinubu ya gana da ministoci biyu game da batun sabon mafi ƙarancin albashi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Gwamnatin tarayya na ci gaba da tattaunawa da ƴan kwadago da nufin cimma matsaya bayan sun janye yajin aikin da suka fara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262