"Ba Addu'a Ba Ce": Malamin Addini Ya Bayyana Abin da Zai Sa a Samu Sauki a Najeriya

"Ba Addu'a Ba Ce": Malamin Addini Ya Bayyana Abin da Zai Sa a Samu Sauki a Najeriya

  • Primate Babatunde Elijah Ayodele ya bayyana cewa addu'a da azumi ba za su ceto ƴan Najeriya daga halin ƙuncin da suka tsinci kansu a ciki ba
  • Shugaban na cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya bayyana cewa shugabanni suka jefa ƙasar nan cikin mawuyacin hali a yau
  • Ya yi nuni da cewa ƴan Najeriya na shan wuya ne saboda yin biris da suka yi da gargaɗin da ubangiji ya yi musu na kada su sake zaɓen jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya ce azumi da addu’o’i ba za su iya magance matsalar tsadar rayuwa a Najeriya ba.

Malamin addinin ya bayyana cewa shugabanni sune suka jefa ƙasar nan a halin da ta tsinci kanta a ciki.

Kara karanta wannan

"Mafita 1 ta rage," Babban malamin addini ya taɓo ciwon da ya fi damun ƴan Najeriya

Primate Ayodele ya gargadi 'yan Najeriya
Primate Ayodele ya ce addu'a ba za ta magance halin da ake ciki a Najeriya Hoto: Elijah Ayodele
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ce Primate Ayodele ya bayyana hakan ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane kuskure ƴan Najeriya suka yi?

Primate Ayodele ya bayyana cewa Allah ba ya sauraron ƴan Najeriya a kan matsalar ƙuncin rayuwa saboda mutane sun zaɓi shugabannin da a yanzu ke sanya su cikin wahala, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun kasa sauraron gaskiya kuma Allah ba zai taimaki ƙasar nan wajen magance matsalar tattalin arziƙi ba idan shugabanni ba su yi abin da ya dace ba.

Tsadar rayuwa: Ƴan Najeriya sun kauce hanya

Ya bayyana cewa duk wanda ya ce ƴan Najeriya su yi addu’a domin samun sauƙin halin wahala da ake ciki to yaudarar kansa kawai yake yi.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya fadi dalilin da ya sa 'yan Najeriya suka tsinci kansu cikin tsadar rayuwa

"Mun kasa bin gaskiya, duk wanda ya ce a yi addu’a domin a magance tsadar rayuwa, yaudarar ƴan Najeriya kawai yake yi. Allah ba ya sauraron ƴan Najeriya a kan lamarin tsadar rayuwa."
"Ba mu sauraron gaskiya kuma mun yi nisa da ita. Allah ba zai sauko ya gyara mana abubuwa ba, abubuwa na taɓarɓarewa amma Allah ba zai taimake mu ba."

- Primate Babatunde Elijah Ayodele

Malamin addinin ya bayyana cewa Allah ya gargaɗi ƴan Najeriya da ka da su zaɓi wata gwamnatin APC a bara amma ba su ji ba.

Saboda haka faston ya ce ƴan Najeriya na shan wuya ne saboda rashin yin biyayya.

Ayodele ya shawarci shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Primate Babatunde Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritua da ke Legas, ya ce dole ne Shugaba Bola Tinubu ya inganta tattalin arziki da tsaro.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami ya fadi nadamarsa kan mika mulki a hannun farar hula

Malamin addinin ya kuma buƙaci shugaban kasar da ya cika alkawarin da ya yiwa ‘yan Najeriya na cewa gwamnatinsa za ta sake fasalin ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng