“Kar A Yi Gaggawan Kiran Jariri Mummuna”: Wata Uwa Ta Saki Bidiyon Sauyawar Danta

“Kar A Yi Gaggawan Kiran Jariri Mummuna”: Wata Uwa Ta Saki Bidiyon Sauyawar Danta

  • Wata uwa ta saki hoton danta yayin da ya sauya gaba daya cikin shekaru, kuma ya sace zuciyar mutane
  • Da take baje kolin sauyawar da ya yi, ta bukaci mutane da kada su dunga kiran jarirai da mummuna a lokacin da aka haife su
  • Jama'a sun garzaya shashin sharhi don nuna sha'awarsu tare da yaba haduwar yaron

Wata yar TikTok @sommywhiteorganics ta girgiza intanet bayan ta saki hotunan sauyawar danta masu ban mamaki.

Uwan dan wacce ke cike da farin ciki ta saki hoton yaron yana jinjiri da kuma wani hotonsa yayin da ya fara girma.

Yaro yana jinjiri da bayan ya girma
“Kar A Yi Gaggawan Kiran Jariri Mummuna”: Wata Uwa Ta Saki Bidiyon Sauyawar Danta Hoto: @sommywhiteorganics/TikTok.
Asali: TikTok

Uwa ta shawarci mutane da kada su yarda su aibata jariri

Yayin da take wallafa bidiyon, ta rubuta wani sako mai taba zuciya, tana mai bukatar mutane da kar su aibata jinjiri da siffar da ya zo duniya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yan Mata Fiye Da 10 a Kan Babura Ya Girgiza Intanet, Sun Jeru Sanye Da Anko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, sauyawar jarirai yana matukar ba kowa mamaki, yayin da ta baje kolin kyawun danta shekaru bayan haihuwarsa.

Ta rubuta:

"Ku dan dakata kafin ku kira yarona da mummuna saboda sauyawarsa zai ba ku mamaki. Dan kyayyawan saurayina!"

Jama'a sun yi martani

@Chi Brandy ta ce:

"Wannan kamannin na farko saboda wahalar da suke sha yayin haihuwa ne."

@user19294302886812 ta yi martani:

"Hadadden yaro."

@Ssmartp247 ta ce:

"Na rantsare labarin dana na fari. hahahhahahahahaahha.”

@user48585179643555 ta yi martani:

"Kyakkyawa."

@Laura ta ce:

"Wow kyakkyawa."

Kalli bidiyon a kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng