"Ka Daina Amince Wa da Kudirori Ba Tare da Sanin Mu Ba" Sanatoci Ga Akpabio
- Sanatoci sun fara yi wa shugaban majalisar dattawa bore kan zartar da kudirori ba tare da saninsu ba
- Sanata Ali Ndume ya caccaki Godswill Akpabio kan amince wa da kudirori ba tare da karanta su a gaban sauran mambobin majalisa ba
- Ogoshi Onawo, Sanatan PDP daga jihar Nasarawa ya koka kan cewa matakin Akpabio ba zai haifar da ɗa mai ido ba
FCT Abuja - Ga dukkan alamu rigima na neman ɓarke wa tsakanin wasu Sanatoci da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Vanguard ta tattaro.
Sanata Ali Ndume, ya caccaki Akpabio, kan amincewa da wasu kudurorin zartarwa ba tare da neman shawarar sauran mambobin majalisar dattawan ba.
Yadda Sanatoci suka fara nuna fushinsu
Ndume, mai wakiltar mazaɓar Borno ta kudu ya nuna rashin jin daɗinsa bisa yadda shugaban majalisar ke tafiyar da wasu kudirorin ba tare da bai wa Sanatoci damar tofa albarkacin bakinsu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani faifan bidiyo da ya watsu daga ranar Alhamis, an ji Ndume na sukar shugaban majalisar dattawa bisa zartar da wasu kudirori ba tare da karanta su a zauren ba.
A cewarsa, Akpabio na amince wa da irin waɗan nan kudirorin ba tare sauran mambobin majalisar sun bada gudummuwa ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Haka nan kuma Sanata Ogoshi Onawo na PDP daga jihar Nasarawa, ya ƙalubalanci Akpabio kan yunkurinsa na zartar da wasu kudirori cikin gaggawa.
Sanatan ya ce:
"Kudirori masu matuƙar muhimmanci sun iso zauren majalisa kuma ana sa ran a amince da su da sauri kamar ƙiftawar haske, wanda ba abu ne mai kyau ga ƙasa ba."
“Kowane Sanata a nan ya kamata a masa bayani, ya gudanar da bincikensa kuma ya bada gudunmawa mai kyau, amma yanayin da za a kawo kudirorin kuɗi kuma a ce cikin awa biyu za a amince da su, ba zai wa ƙasa kyau ba."
"Yallabai, yau kana kan wannan kujera, tarihi zai hukunta ka da cewa abubuwa irin wannan ba su da amfani ga kasar nan.”
Sanata Akpabio ya maida martani
Amma da yake maida martani ga kalaman Sanata Onawo, Akpabio ya ce:
"Idan kudurorin da muka zartar suna da amfani ga kasa, tarihi zai mun daidai. Ba na jin mun zo nan ne mu zartar da wani kudirin doka da bai dace da muradun ‘yan Nijeriya ba. Don haka, na ɗauki kokenku."
Gwamnatin Kano Ta Aike da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Sanata Bello Yusuf
A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya fitar sanarwan ta'aziyya bisa rasuwar Sanata Bello Maitama Yusuf.
Abba ya ce rashin babban mutum mai ƙima a idon jama'a kamar Sardaunan Dutse babban giɓi ne da cike shi ka iya zama ƙalubale.
Asali: Legit.ng