An Nada Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ekweremadu, a Matsayin Kwamishina

An Nada Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ekweremadu, a Matsayin Kwamishina

  • Gwamna Peter Mbah na Enugu ya mika jerin sunayen kwamishinoni 15 gaban majalisar dokokin jihar domin ta tantance tare da tabbatar da su
  • Lloyd Ekweremadu, dan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya samu shiga cikin jerin kwamishinonin
  • Haka kuma, Gwamna Mbah ya zabi diyar tsohon gwamnan jihar, Sullivan Chime a kwamishinonin nasa

Jihar Enugu - Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya zabi Lloyd Ekweremadu a matsayin daya daga cikin kwamishinoni 15 a jihar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Lloyd ya kasance da ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, wanda ya aka yankewa hukunci tare da matarsa, Beatrice da likitansu, Obinna Obeta, a kotun kasar Birtaniya kan safarar sassan jikin mutum.

An nada dan Ekweremadu kwamishina
An Nada Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ekweremadu, a Matsayin Kwamishina Hoto: The Guardian
Asali: UGC

An nada diyar tsohon gwamna kwamishina

Mbah ya kuma zabi Ada Chukwu, diyar tsohon gwamnan jihar, Sullivan Chime cikin kwamishinoninsa.

Kara karanta wannan

Tausayin talaka: Zulum da wasu gwamnoni 2 sun kawo hanyar rage radadin cire tallafi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin majalisar, Uche Ugwu ne ya karanto jerin sunayen a zauren majalisar a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli.

A wata wasika da aka rako jerin sunayen, Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Chidiebere Onyia, ya ambaci cewa ba lallai ne wannan ya kasance jerin sunayen karshe ba sannan ya bukaci majalisar da ta duba sunayen cikin gaggawa.

Onyia ya ce:

"Yayin da ba lallai ne wannan ya zama cikakken jerin sunayen ba, ina da yakinin cewa wannan bukatar zai samu la'akarinku cikin gaggawa."

Daga cikin zababbun kwamishinonin 15 akwai shahararren mai watsa shirye-shirye Aka Eze Aka, Farfesa Ndubueze Mba, Misis Ngozi Eni, Farfesa Sam Ugwu, Chika Ugwoke da Dr Kingsley Ude.

Sauran sun hada da tsoffin kwamishinoni; Farfesa Emmanuel Obi da Deacon Okey Ogbodo, Da kuma Misis Ugochi Madueke, Dr Malachy Agbo, Gerrald Otiji, Nathaniel Urama, da Prince Lawrence Ezeh, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Ajiye Zababben Kwamishina Da EFCC Ta Gurfanar

Gwamnatin Kano ta soke lasisin yan masana'antar Kannywood

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ta soke gaba daya lasisin yan masa'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba Almustapha, ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatin jihar daukar wannan makali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng