Matashiya Ta Dasa Kamarar Sirri a Gaban Gidanta, Ta Kama Makwabciyarta Tana Yi Mata Sata

Matashiya Ta Dasa Kamarar Sirri a Gaban Gidanta, Ta Kama Makwabciyarta Tana Yi Mata Sata

  • Wata matashiya da ke zargin cewa makwabciyarta na yi mata sata ta dasa kamarar CCTV saboda tsaro
  • Ba tare da sanin cewa tana kallonta ba, makwabciyar ta tunkari kofar matashiyar sannan ta ake daukar wani kunshi
  • Yan sakanni a bidiyon da ya yadu, matashiyar ta tunkari matar sannan ta nuna mata bidiyonta da ta nada

Wata matashiya ta wallafa wani bidiyo da ke nuna lokacin da ta kama makwabciyarta wacce ke yawan yi mata satar kayayyakinta.

Domin kamata tana aika-aikar, matashiyar ta dasa wani kamarar sirri a gaban kofarta. A farkon bidiyon, an gano makwabciyar tana daukar kunshin kayan da ba nata ba daga bakin kofar matashiyar.

Budurwa ta kama makwabciyarta tana sace mata kaya a bakin kofa
Matashiya Ta Dasa Kamarar Sirri a Gaban Gidanta, Ta Kama Makwabciyarta Tana Yi Mata Sata Hoto: @kenntoliv
Asali: TikTok

Kafin ta dauka, sai da ta dudduba gaban da arewa, kudu da yamma don tabbatar da babu mai kallonta. Jim kadan bayan ta yi aika-aikar, matashiyar ta bayyana, tana tambayarta dalilinta na daukar mata kaya.

Kara karanta wannan

“Na Fi Mijina Samun Kudi”: Matar Aure Ta Ce Bata Bude Asusun Hadin Gwiwa Ba a Gidan Aurenta

Da fari matar ta karyata har sai da ta nuna mata bidiyon lokacin da ta dauki kayan. Tana ta inda-inda cikin rudani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Ok_n_what ta ce:

"Ganin cewa mutane na sace kunshin kaya ba tare da masaniya kan abun da ke ciki ba akwai matukar rikitarwa."

Abby Morland ta ce:

"Ba zan iya yarda da wannan ba! Na ji dadin cewa kin tsayawa kanki."

Harvey ta ce:

"Abu mafi wahala a tarihi."

Darryl Moss ya ce:

"An kama ta dumu-dumu."

Fungalk1 ta tambaya:

"Shin dawo da shi?"

Leena ta ce:

"Ina da makwabciya da ta sace mun kaya da ya kai 200€ har yanzu bani da masaniya kan ko wacece."

jonathanwillis299 ya ce:

"Idan makwabcina ya dauki wani abu na son don ya adana shi ne."

d4n1337 ya ce:

Kara karanta wannan

Budurwa Yar Shekaru 19 Wacce Ta Tara Kudi Don Siyan Siminti Da Bulo Ta Gina Daki 1, Ta Sa Kayan Alatu

"Wannan tsarin kai sako bai yi ba. A kasata idan mai kai sako ya iso zai kiraki a waya ya ga ko kina gida. Idan ba kya nan zai je ya dawo."

Peter Obi Ya Jinjinawa Ma’aikaciyar Otel Da Ta Mayarwa Kwastama Da Miliyan 55

A wani labari na daban, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya jinjinawa ma'aikaciyar otel din 'Eko Hotel and Suites', wacce ta mayarwa wani kwastama kudin naira miliyan 55 ($70,000) da ya manta.

An tattaro cewa ma'aikaciyar otel din mai suna Ms Kekwaaru Ngozi Mary, ita ce ta tsinci kudin a da bakon otel din ya batar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng