Tallafin Tinubu: “Rabon N8,000 Duk Buge Ce” – In Ji Gwamnan Kaduna, Uba Sani
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya kira shirin gwamnatin tarayya na rabawa yan Najeriya kudi a matsayin yaudara
- Sani a wata hira da aka yi da shi ya yi watsi da matakin inda ya ce an tsame kaso 70 zuwa 75 na mutanen karkara a arewa maso yamma daga shirin tallafin gaba daya
- Gwamnan na APC ya kara da cewar daga gogewarsa a matsayin ciyaman na kwamitin bankuna na shekaru hudu a majalisar dattawa ta tara shakka babu shirin yaudara ce
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana shirin bayar da tallafin kudi na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin yaudara.
Gwamnatin Tinubu ta ba da shawarar rabawa iyalai miliyan 12 N8,000 na tsawon watanni shida don rage masu radadin cire tallafin man fetur da aka yi, shirin da aka jingine daga baya bayan ya sha suka daga yan Najeriya.
Gwamnan Kaduna Uba Sani ya ce shirin raba N8,000 duk bige ce, ya fadi dalili
Da yake magana a wata hira da Arise TV a daren ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli, Sani ya bayyana cewa babu wani sahihin bayanai na wadanda za su amfana daga shirin, jaridar Punch ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan ya ce:
"Matsayina a kodayaushe ya kasance cewa, a wannan mawuyacin lokaci, kada batun raba kudi ya zama abun da za mu kawo cikin lissafi. Ina ganin shirin rabon kudi a ganina, a ra'ayina, damfara ce. Yaudara ce gaba daya. Zan iya tabbatar da hakan sosai, saboda wa kuke tura wa kudin?”
Sai dai kuma, gwamnan ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta fara tabbatar da ganin cewa an kula da mutanen da aka tsame daga cikin shirin kudin musamman a arewa maso yamma sannan a kawo tsarin kudi kafin aiwatar da shirin bayar da tallafin kudin, rahoton Vanguard.
"Mu kara zuba karin kudi don mu tabbatar mun bude musu asusu, mu sanya su a ciki, idan ba mu yi haka ba, duk abin da muka yi duk yadda ka yi, kudin zai shiga hannun mutanen da ba su dace ba, gaskiyar magana ke nan,” inji shi.
"N8,000 Kudi Ne Masu Yawa" Gwaman Sule Ya Kare Tallafin Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya kare shirin gwamnatin tarayya na raba wa magidanta N8,000 domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur a Najeriya.
Gwamna Sule ya yi ƙarin haske kan tallafin N8,000 ne yayin da ya bayyana a cikin shirin siyasa a yau na kafar watsa labaran Channels tv ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng