Gasar Kuka: Shehu Sani Ya Caccaki GWR Kan Dan Najeriya Da Ya Makance
- Sanata Shehu Sani ya caccaki kundin banjinta na Guinness sannan ya kuma dasa ayar tambaya kan ka'idojinsu na shiga gasar
- Tsohon dan majalisar na Najeriya ya ce akwai bukatar kungiyar ta kasa da kasa ta nemi samun bayanan lafiyar mutumin da ke son shiga gasar
- Ya fadi hakan ne a wani rubutu da ya yi a Twitter yayin da yake martani da makancewar da wani dan Najeriya ya yi lokacin da yake kokarin yin gasar kuka
Tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani ya shiga sahun yan Najeriya wajen yin martani ga mummunan al'amarin nan inda wani matashi ya makance a kokarinsa na shiga kundin bajinta na Guinness.
Dan Najeriyan mai suna Tembu Ebere, ya yi kokarin shiga kundin bajinta na Guinness ta hanyar kuka na tsawon kwanaki bakwai ba tare da ya dakata ba.

Kara karanta wannan
Dan Najeriya Ya Makance Yayin da Yake Kokarin Shiga Kundin Bajinta Na Guinness Ta Hanyar Kuka Na Kwanaki 100

Source: UGC
Ebere, a wata hira da BBC a ranar Lahadi, ya bayyana cewa ya makance na tsawon mintuna 45 yayin da yake kokarin gasar.
Ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Sai da na sauya dabara sannan na rage kukana."
Gasar kuka: Shehu Sani ya caccaki kungiyar 'Guinness World Record'
A daya bangaren, Sanata Sani ya yi kira ga kungiyar GWR da ta nemi kwafin bayanan lafiyan duk wadanda ke son shiga gasa kafin su barsu su ci gaba da gasar.
A wani rubutu da Legit.ng ta gani a Twitter, Shehu Sani ya rubuta:
"Ya kamata kungiyar Guinness World Record ta bukaci samun bayanan lafiyar masu niyar shiga gasarta duba ga fargaba da takurar da masu gasar ke sanya kansu a ciki don shiga kundin bajintar. Bai kamata a yi watsi da lafiyar mutum ba saboda hatsarin da ke tattare da abun."

Kara karanta wannan
Yanzu: COEASU Ta Umarci Mambobinta Su Na Zuwa Aiki Na Kwanaki 2 Kadai A Sati Bayan Cire Tallafi
Ya kuma bukaci kungiyar GWR ta yi watsi da duk mai shiga gasar da baida cikakken lafiya tare da yin la’akari da kyawawan dabi’unsu.
Ya ce:
"Ya kamata @GWR ta yi watsi da duk mutumin da bai da lafiyar jiki ko na kwakwalwar da zai iya daukar wannan hatsari. Wannan kuma lamari ne na dabi'a.
"Ya kamata rahoton wani dan Najeriya da ya yi kuka har sai da ya makance ya zama dalilin bukatar binciken lafiya da kwakwalwar mutum kafin ya shiga gasa.
"Bai kamata @GWR ya zama dandamalin kisan kai ba."
Dan Najeriya na shirin auren surukarsa bayan mutuwar matarsa
A wani labari na daban, wani magidanci na neman auren surukarsa (uwar matarsa) shekaru biyu bayan mutuwar matarsa.
A labarin da Azuka Onwuka ya wallafa a Facebook, mutumin ya ce gwanda ya auri mahaifiyar matarsa sannan ya guji kawo wata daga waje.
Asali: Legit.ng