Arzikin Dangote, Rabiu, Adenuga Ya Ragu Da Sama Da Biliyan 423 Cikin Awanni 24
- Manyan attajiran Najeriya Aliko Dangote, Rabiu Abdulsamad da Mike Adenuga sun samu raguwa a arzikinsu
- A dunkule, mutum uku da suka fi kowa kudi a Najeriya sun samu raguwar sama da naira biliyan 423 a arzikinsu cikin awanni 24 kacal
- Tun bayan faduwar darajar Naira a hukumance, arzikin manyan attajiran uku ya yi kasa sosai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Manyan attajiran Najeriya kuma shahararrun yan kasuwa, Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu, da Mike Adenuga, sun samu raguwar naira biliyan 423 (dala miliyan 529) a dukiyarsu cikin awanni 24 da suka gabata.
Binciken da Legit.ng ta yi kan kididdigar da mujallar Forbes ta fitar ya nuna cewa Rabiu ya fi kowa asara a tsakanin attajiran uku.
Shugaban kamfanin BUA yana kallo dukiyarsa ta ragu da dala miliyan 335 (naira biliyan 267.8) zuwa dala biliyan 5.3 a ranar Talata, 18 ga watan Yuli.
Duk da tarin raguwar da ya samu, Forbes ta sanya Rabiu a matsayin mutum na 528 cikin masu kudin duniya a ranar Talata kuma yana kan matsayinsa na biyu a cikin masu kudin Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Raguwar arzikin Dangote
A banaren Aliko Dangote, dala miliyan 185(naira biliyan 147.93) ne ya ragu a arzikinsa, wani cikas ga kokarinsa na rike inkiyar da ake masa na mai kudin Afrika.
Forbes ta rahoo cewa a ranar Talata, Dangote na da arzikin da ya kai dala biliyan 10.1 kuma yana nan a matsayin mutum na biyu a masu kudin Afrika, a bayan Johann Rupert a Afrika wanda arzikinsa ya kai dala biliyan 11.7.
Mike Adenuga
Mutum na uku cikin wadanda suka fi kowa kudi a Najeriya, Mike Adenuga shine kasa a raguwar arzikin da attajiran uku suka samu.
Arzikinsa ya ragu zuwa dala biliyan 3.2 bayan ya rasa dala miliyan 9 (naira biliyan 7.12) a ranar Talata.
A cewar Forbes, Adenuga wanda ya gina arzikinsa kan harkokin sadarwa da mai shine mutum na 833 cikin masu kudin duniya a yanzu.
Elon Musk ya dawo na daya a masu kudin duniya
A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa Mai kamfanin Twitter, Elon Musk ya dawo matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a duniya bayan asarar $200bn a shekara daya.
Musk ya rike matsayin nasa ne bayan adadin kudin da ya ke da shi ya kai har $250bn a jerin masu kudin duniya da mujallar Forbes ta sake.
Asali: Legit.ng