Yar'Adua, Alamieyeseigha, Da Wasu Takwarorin Shugaban Kasa Tinubu Da Suka Kwanta Dama
Shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi bakuncin wasu takwarorinsa da aka zabe su tare a matsayin gwamnoni a shekarar 1999 a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.
Najeriya ta koma mulkin damokradiyya a 1999 bayan shafe tsawon shekaru 16 na mulkin soja, kuma shugaban kasa Tinubu na daya daga cikin zababbun gwamnonin wannan lokacin.
Shekaru 20 bayan zaben, tsoffin gwamnonin sun dauki hanyoyi daban-daban a rayuwa, kuma akalla 10 daga cikinsu sun kwanta dama a cikin shekarun bayan zabensu na 1999.
Ga jerin wadanda suka rasu a kasa:
Chinwoke Mbadinuju
An zabi Mbadinuju a matsayin gwamnan jihar Anambra a shekarar 1999 kuma ya rike mukamin ne na wa'adi daya kacal.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya rasu a ranar 11 ga watan Afrilun shekarar nan a asibitin kasa da ke Abuja bayan yar gajeruwar rashin lafiya.
Diepreye Alamieyeseigha
An zabe shi a matsayin gwamnan jihar Bayelsa sau biyu karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma yana cikin rukunin gwamnonin 1999 amma aka tsige shi kan tuhumar rashawa.
Alamieyeseigha ya mutu a 2015 a asibitin kotarwa na Port Harcourt bayan zuciyarsa ta buga.
Mala Kachalla
An zabi Kachalla a matsayin gwamnan jihar Borno a 1999 karkashin inuwar jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), daga baya ya koma jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) amma ya fadi a shirinsa na tazarce a 2003.
Ya rasu a gidansa da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno yana da shekaru 66 a 2007 bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Abubakar Hashidu
Hashidu na cikin wadanda suke yi nasarar darewa kujerar gwamna bayan dawowar damokradiyya a 1999.
An zabe shi a matsayin gwamnan jihar Gombe a 1999 da 2003 sannan ya rasu a ranar 27 ga watan Yulin 2018 bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Umaru Yar’Adua
Ya yi aiki a matsayin gwamnan jihar Katsina sau biyu da kafa tarihi a matsayin gwamna na farko da ya bayyana kadarorinsa.
Yar'Adua ya gaji tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban kasar Najeriya amma bai dade ba ya fara rashin lafiya. Ya rasu a 2010.
Abubakar Audu
Audu ya kasance gwamnan farar hula na farko a jihar Kogi a 1992, amma mulkinsa ya samu tangarda saboda kwace mulki da soji ta yi a 1993.
Da dawowar damokradiyya a 1999, an zabi Audu a matsayin gwamnan jihar sannan ya mutu a ranar 22 ga watan Nuwamban 2015.
Abdulkadir Kure
Kure ya kasance gwamnan jihar Neja sau biyu tsakanin 1999 da 2000 karkashin inuwar jam'iyyar PDP sannan ya yi suna saboda kafa dokar shari'a a jihar.
Ya rasu a ranar 8 ga watan Janairun 2017 a kasar Jamus yana da shekaru 60 a duniya.
Lamidi Adesina
Kamar yadda aka fi kiransa da Lam Adesina, an zabe shi domin yi wa mutanen jihar Oyo hidima a 1999.
Tsohon gwamnan na jihar Oyo ya rasu a watan Nuwamban 2012 a wani asibiti mai zaman kansa a jihar Lagas.
Mohammed Lawal
Lawal ya kasance tsohon gwamnan jihar Kwara da aka zaba a 199 karkashin inuwar jam'iyyar All Peoples Party amma a kokarinsa na zargewa zai ya sha kaye a hannun tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a 2003.
Tsohon gwamnan ya rasu a watan Nuwamban 2006 a wani asibitin Landan bayan ya yi dan jinya.
Adebayo Adefarati
An zabi Adefarati a matsayin gwamnan jihar Ondo a 1999 karkashin inuwar jam'iyyar AD, jam'iyyar da a cikinta ne aka zabi Tinubu a matsayin gwamnan jihar Lagas.
Ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AD a 2007 amma ya rasu yan makonni kafin zaben yana da shekaru 76.
Ban taba sanin zan zama shugaban kasa ba, Tinubu
A baya mun ji cewa tsohon hugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai taba sanin cewa zai dare kan kujera ta daya a kasar ba, jaridar Daily Trust ta rahoto.
A cewar kakakin shugaban kasar, Dele Alake, Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga rukunin gwamnonin 1999 a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng