“Na Ga Wata Bakar Halitta”: Matashi Da Ya Sunkuya a Kasuwar Lagas Ya Fadi Abun Da Idanunsa Suka Gane Masa

“Na Ga Wata Bakar Halitta”: Matashi Da Ya Sunkuya a Kasuwar Lagas Ya Fadi Abun Da Idanunsa Suka Gane Masa

  • Wani matashi dan Najeriya ya magantu game da arangamar da ya yi bayan ya sunkuya a wata kasuwar Lagas
  • Kafin wannan ranar, ya yi kokarin sunkuyawa a kasuwar don gane ko da gaske ne zai ga abubuwan ban mamaki amma sai ya ga akasin haka
  • A kokarinsa na uku, matashin ya ce ya kusa haukacewa bayan ya ga wata bakar halitta, halittu marasa kafa da wasu masu kawuna biyu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi dan Najeriya mai suna Umuefe Godswill Oluwaseun James, ya bayyana arangamar da ya yi a kasuwar Lagas don tabbatar da ikirarin da ake yi cewa ba kowa ne mutum ba a kasuwar.

A wata wallafa da ya yi a Twitter, mai wakar yabon ya ce ya ga abubuwa da idanunsa bayan ya sunkuya a kasuwar Iyana Ipaja, Lagas a 2016.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida: Za a Tura Naƙasassun jihar Kano Zuwa Jami’o’in Kasashen Waje

Wnai matashi ya ga abubuwan ban tsoro a kasuwa
“Na Ga Wani Bakar Halitta”: Matashi Da Ya Sunkuya a Kasuwar Lagas Ya Fadi Abun da Idanunsa Suka Gane Masa Hoto: Guardian Nigeria
Asali: UGC

Kafin arangamar da ya yi a 2016, Godswill ya ce ya fara kokarin sunkuyawa a kasuwar yana a JSS 2 bayan dan ajinsu ya basu labarin cewa akwai wasu halittu masu ban tsoro a kasuwar. Ya ce bai ga komai ba.

Lokacin da suka kara tattaunawa a babban sakandare, Godswill ya ce ya sake kokarin gwadawa a kasuwa amma ya sha kunya. Sai dai azarbabinsa ya kara kaishi ga gwadawa a 2016, duk da yan kasuwa mata da direbobin mota sun gargade shi a kan haka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Godswill ya yi arangama da wasu halittu masu ban tsoro

A cewar Godswill, koina ya yi shiru lokacin da ya sunkuya inda ya yi kamar zai ajiye makulansa ne.

Da farko, matashin ya ce ya ga wata bakar halitta da ke da jiki kamar na macijiya tana doso inda yake. Sai ya gaggauta daga kansa cike da tsoro, amma a nan ne ya fara cin karo da karin abubuwan ban tsoro.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara da Kyau Amma Tun Farko na San Babu Inda Buhari Zai Je - Dattijon Arewa

Lokacin da ya daga kansa, Godwill ya ce ya gano cewa duk mutanen da ke kewaye da shi ba mutane bane. Godswill ya bayyana cewa wasu mutane sun siyar da kayansu ga halittu marasa kafafuwa, ya ce wasu na da kawuna biyu wasu kuma farare ne.

Godswill ya ce ya dawo hayyacinsa ne bayan wani ya taba shi. Ya bayyana cewa abun da ya gani shine masomar matsalarsa ta rashin bacci. Lamarin ya kusa haukatar da shi.

Kalamansa:

"Wasu sun kasance tsirara sannan wasu na sanye da dogayen kaya da baka iya ganin hannaye da kafafuwansu.
"Wasu na sanye da fararen kaya yayin da wasu ke kama da dabobbi da jiki iri-iri!!
"Yooo na kusa haukacewa saboda na cika da tsoron abubuwan da na gani gaba daya.
"Kamar duk abubuwan sun faru ne cikin yan mintoci."

Jama'a sun yi martani

@FriendlyOgba ya ce:

"Wannan na sunkuyawar ya yi nisa, idan kana da kare ka tashi da karfe 6 akwai wani abu kalar dorawa a idanunsu ka cire sannan ka sanya a idonka sai ka tafi kasuwa da karfe 2pm, abun da idanunka za su gani kada ka fada idan ba haka ba ka tafi kenan...wannan ne dalilin da yasa baka ganin karnuna a kasuwa da rana."

Kara karanta wannan

Rikici Yayin Da Mai Kara Ya Fashe Da Kuka Ya Na Nema Wa Wanda Ya Ke Kara Alfarma, Ya Fadawa Kotu Dalilansa

@dejiaso ya ce:

"Akwai wannan kasuwar mai ban tsoro a Ikorodu ma, ya fi kama da kauye, yanayin ya banbanta da sauran yankunan Ikorodu, ban tuna sunanta ba amma ranar da na shiga wajen na kasa samun sukuni kwata-kwata."

@segunDaniel22 ya ce:

"Wanda na sani na fasto ne a nan kasuwar Odogugan. Faston na yawan addu'an Allah ya bude masa idanu ya ga abubuwa.
"A ranar da Allah ya bude masa idanu a ranar ne wannan faston ya tafi kasuwar Odoguyan...a cewar mutane, mutumin ya fadi sannan ya mutu."

Matashi ya bar makaranta ya je bibiyar tsohuwa, mahaifinsa ya kama shi a bidiyo

A wani labarin kuma, wani bidiyo da ya yadu ya nuno wani matashi dan Najeriya mai shekara 20 wanda ya bar makaranta domin tarewa da wata hajiyar birni mai kudi.

A bidiyon, mahaifin yaron ya nuna rashin jin dadinsa game da halin yaron nasa, yana mai cewa ya so dansa ya je makaranta amma maimakon haka, ya zabi bin wacce ta isa ta haife shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng