Matashi Ya Baje Kolin Janaretonsa Mara Amfani Da Fetur, Da Hasken Rana Yake Aiki Kuma Baya Kara
- Wani dan Najeriya ya baje kolin setin janareto da baya aiki da man fetur kuma baya kara
- A cewarsa, janareton mara amfani da fetur kuma mara kara zai iya daukar kwamfutar laftof, kayan wuta da farin kwan fitila
- Ya ci gaba da bayyana hanyoyi biyu da za a iya cajinsa, abun da ya ba mutane da dama da suka nuna sha'awar mallakarsa mamaki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani matashi dan Najeriya ya maje kolin wani janareto mai amfani da hasken rana da baya bukatar man fetur.
A wani bidiyon TikTok, ya yi amfani da janarfeton wajen kunna wasu kayan wuta sannan ya bayyana cewa yana da karfin 500-watt.
Kan yadda za a iya cajinsa ya ce janareton na da hanyoyi biyu da ake iya cajinsa. Daya shine ta hasken rana sannan dayan ta lantarki.
“Na Rasa Matata Da Yara 5”: Matashiy Ya Taimaki Wani Tsoho Da Ke Yawon Bara a Titi a Bidiyo Mai Tsuma Zuciya
Ya ba jama'a damar kallon yadda yake aiki sannan ya baje kolin wasu kayayyakin wuta da yake dauka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mutane da dama sun so sanin nawa mutum zai kashe wajen mallakar guda daya.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun nuna sha'awar mallakar janareton
Jude Moore ya ce:
"Menene karfin aikinsa, shin za a iya cajinsa da wutar lantarki idan babu panel kuma nawa yake don Allah?"
BigZiko1 ya ce:
"Sai ku sanya kaya mutum ya yi ta tambayan farashi amma ku yi gum ba za ku amsa ba toh menene amfanin sakawa idan ba za ku amsa tambayoyin kwastamomi ba?"
user1675960799865 ya ce:
"Firinji nawa zai iya dauka? zai iya daukar injin wanki da na jan ruwa??? Garantin shekaru nawa?"
inyamasylvester ya ce:
"Nawa ne kuma awa nawa zai iya yi."
Bidiyon Yadda Amarya Ta Zubawa Ango Abinci Yayin da Take Kokarin Manna Masa ‘Kiss’ Ya Girgiza Intanet
Mroctopus ya ce:
"Duk wadannan ba sune karshen matsalar ma'aikatar lantarki ba kawai dai mafita ne, shugabanninmu sun lalata kasar nan."
Matashi ya sauya motarsa zuwa mai amfani da gas, da kudi kadan yake cika tanki
A wani labarin, mani matashi dan Najeriya ya nunawa mutane yadda yake amfani da motarsa ba tare da damuwa da tsadar mai ba.
Da yake baje kolin injin dinsa wanda aka sauya zuwa mai amfani da iskar gas, mutumin ya dauki motar zuwa gidan mai domin siyan gas. Ya bayyana cewa ba zai kashe fiye da N2000 ba wajen cika tankin.
Asali: Legit.ng