Yadda Wadanni Suka Taru a Waje Guda Domin Yin Kus-Kus, Sun Tika Rawa a Bidiyo
- Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wadanni da dama da suka taru a wuri guda don gudanar da wani taro
- Mai amfani da TikTok, Ben ya wallafa bidiyon da ke nuna lokacin da wadannin ke rawa cike da farin ciki a wajen taron
- Bidiyon ya haifar da martani masu ban dariya daga wajen masu amfani da TikTok wadanda suka jinjinawa karfin gwiwar da wadannin suka nuna a bidiyon
Wani mai amfani da TikTok ya wallafa wani bidiyo da ke nuna lokacin da wata kungiya ta wadanni suke tikar rawa cikin annashuwa da walwala yayin wani taronsu.
Mai shafin wanda aka bayyana da suna Ben ya wallafa wani bidiyo da ya ce an dauke shi ne lokacin da ake wani taro na wadanni.
Bidiyon ya fara da hasko wadanni a filin rawa, suna karkada jikinsu cike da annashuwa da walwala.
Bidiyo ya nuno wadanni suna rawar wakar Buga na Kizz Daniel
Suna ta rawar wakar Buga wanda wani shahararren mawakin Najeriya, Kizz Daniel ya rera.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Akwai wadanni maza da maa a wajen kuma kowannensu na ta baje bajintarsa a filin rawa.
Wurin ya kaure da jin dadi yayin da wadannin suka hadu da kuma yin rawa cike da karfi da kuzari. Ba a bayyana wajen da taron ya gudana ba.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Bidiyon ya haifar da martani masu ban dariya tsakanin masu amfani da TikTok. Mutane da dama sun ce abu ne mai kyau ganin cewa wadanni sun hadu don ganawa a tsakaninsu.
@desire97 ta ce:
"Nagode Allah da wannan tsayi nawa na yan Amurka."
@jacksonmunubi720 ya ce:
"Wani kasa kuke zuwa?"
@khemy ya ce:
"Wacce ta sanya farin tufafi."
@Khãïfär Mïllêz Kumãr
"Wato wannan muke kira da dan taron zumunci."
@user MuhammedRabo ya ce:
"Me yasa bana ganin Amanda a nan."
@mapskitis ya ce:
"Karfin gwiwarsu ne ya burge ni."
@estherabafun ta ce:
"Na ji dadin yadda suke cike da karfin gwiwa da alfahari da kasancewarsu mutane na musamman."
Matashiya ta dafa kwai karo na farko a rayuwarta, ya babbake kamar bayan tukunya
A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiya yar masu hannu da shuni ta yi kokarin dafa kwai karo na farko a rayuwarta, amma sai aka yi rashin dace domin dai kwan ya babbake fiye da tunani.
Rike da konannen kwai a hannunta, matashiyar cike da barkwanci ta bayyana yadda ake dafa irin kwanta: "Kawai ka zuba ruwa a kan wuta, sai ka saka kwan a ciki, sannan ka yi bacci."
Asali: Legit.ng