“Wannan Ba Shugabanci Mai Kyau Bane”: An Ba Abba Gida-Gida Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano

“Wannan Ba Shugabanci Mai Kyau Bane”: An Ba Abba Gida-Gida Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano

  • An ba Gwamna Abba Kabir Yusuf wa'adin awanni 72 ya daina aikin rushe-rushe a jihar Kano
  • Kungiyar Good Governance and Change Initiative (GGCI) ce ta bayar da wa'adin a ranar Talata, 20 ga watan Yuni
  • An yi barazanar maka Gwamna Yusuf a kotu idan ya yi watsi da gargadin kungiyar kamar yadda aka tsara

FCT, Abuja - An ba gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, wa'adin awanni 72 ya dakatar da aikin rusau da ke gudana a jihar sannan ya kira wadanda abun ya ritsa da su domin tattaunawa da nufin samun mafita.

Wata kungiyar masu rajin tabbatar da dimokradiyya karkashin inuwar Good Governance and Change Initiative (GGCI) ce ta bayar da wa'adin.

Ganduje da Yusuf
“Wannan Ba Shugabanci Mai Kyau Bane”: An Ba Abba Gida-Gida Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Sun ta rahoto, kungiyar ta yi barazanar kai karar Gwamna Yusuf kotu idan ya ki bin sharuddan wa’adin.

Kara karanta wannan

Rusau: NITP Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Tsagaita Rushe-rushe, Ta Bayyana Irin Asarar Da Aka Tafka

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Talata, 20 ga watan Yuni, shugaban kungiyar GGCI na kasa, Okpokwu Ogenyi, ya ce bai ji dadin yadda gwamnatin jihar Kano mai ci ta fara ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Makonni uku da suka gabata sun zamo tamkar jahannama a jihar Kano inda kake jin kuka a kusan kowani gida da ke birnin Kano. Gwamna Abba Yusuf ya zama inuwar giginya ga shugabanci mai kyau, hatta magoya bayansa basa alfahari da shi a yanzu saboda rashin tausayinsa ga mutanen jihar Kano.
"Ta yaya a cikin kasa da mako guda gwamna zai rusa kadarori da ya kai biliyan dari biyu da shida ba tare da ya yi nazarin tsarin ba balle a kai ga ragewa masu kadarorin radadi?" ya tambaya.

A cewar Ogenyi, mataki na doka ne ya fi dacewa wajen magance lamarin fiye da rushe gine-gine na miliyoyin nairori.

Kara karanta wannan

Ba dai Atiku ba: Gwamnan PDP ya fame tsohon gyambo, ya yabi Wike, ya soki Atiku

Ya ce kamata ya yi a binciki gwamnatin baya wacce ake zargin ta ba da filayen ba bisa ka'ida ba ba wai mutane su sha azaba daga gangancin gwamnatin baya ba, Blue Print ta rahoto.

Kungiyar ta roki Tinubu

Yayin da take ba gwamnatin Kano awanni 72 ta magance rikicin, kungiyar ta roki shugaban kasa Bola Tinubu da ya shiga tsakani sannan ya takewa Abba Yusuf birki.

"Muna kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya gaggauta shiga tsakani sannan ya takewa Abba Yusuf birki don kada ya ci gaba da rusa gine-gine wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka a jihar.
"...Sabida haka mun ba Gwamna Yusuf wa'addin awanni 72 ya saita kansa dannan ya daina rushe-rushen da ke gudana, ya kira mutanen da abun ya shafa ko ya fuskanci hukunci."

Gina Kano Ya Kamata Ayi Ba Rusa Kano Ba” – Ali Madagwal

A wani labarin kuma, mun ji cewa jarumin barkwanci Aliyu Muhammad Idris wanda yafi shahara da sunan Madagwal, ya soki shirin rusau da gwamnatin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida take yi a jihar Kano.

Jarumin ya bayyana cewa babban abun da jihar Kano ke bukata a yanzu shine yadda za a ci gaba da ginata ba wai a rusa ta ba, kamar yadda ya bayyana cewa gwamnatin Abba Ganduje ta yi aiki idan har maganar gaskiya ake so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: