“Kada Ka Saki Nnamdi Kanu”, Asari Dokubo Ga Shugaban Kasa Tinubu
- Tsohon mai fafautuka kuma jigon Neja Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya magantu a kan lamarin shugaban IPOC, Nnamdi Kanu
- Dokubo ya shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya saki Kanu domin fitarsa ba zai haifar da 'ya'ya masu idanu ba
- Ya ce sakin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafiran zai sake tada zaune tsaye ne a kasar
Abuja - Mujahid Asari Dokubo, jigo a yankin Neja Delta kuma tsohon dan tawaye, ya ce sakin shugaban kungiyar yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ba zai saukaka tashin hankalin da ke yankin kudu maso gabashin kasar ba.
Dukubo ya fada manema labarai na fadar shugaban kasa cewa sakin shugaban na IPOB zai kara tada zaune tsaye ne, jaridar The Nation ta rahoto.
Dokubo wanda suka yi ganawar sirri da shugaban kasa Bola Tinubu cikin sirri a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuni a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ya ce a bar Kalu ya fuskanci shari'a.
Jaridar Daily Trust ta nakalto Dokubo yana cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sakinsa zai sake haifar da yanayi na rashin tabbass, a lokacin zanga-zangar Endsars, Nnamdi Kanu na yawo cikin yanci. Me ya yi? Ya sake watsa fetur a wutar Endsars. Yanzu an kama shi. Ya maganar mutanen da suka mutu? Wannan ta'adanci ne. Ya kamata ya fuskanci shari'a.
"Sakin Nnamdi Kanu yanta aikata laifi ne kuma ba da tukwicin kisan mummuke na bayin Allah. Ya kamata ya fuskanci shari'a kan abubuwan da ya aikata da tunzura mutane da ya yi."
Mun dai ji cewa a mako uku da suka gabata, Mista Dakubo, ya tattara matasan Neja Delta kuma ya jagorance su suka halarci zaman Kotun sauraron korafe-korafen zaɓen shugaban ƙasa mai zama a Abuja.
Dokubo wanda ya kasance dan gani kashenin sabon shugaban kasar ya gaya wa 'yan Najeriya cewa su kama shi da laifi idan har gwamnatin Tinubu ta gaza.
Tinubu ya ziyarci Shugaban kasa Tinubu a fadar Villa
A wani labarin kuma, mun ji cewa mai kudin Afrika kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya kai wa shugaban kasa Bola Tinubu ziyarar ban girma.
Tinubu ya karbi bakuncin Dangoten a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng