Ginin Daula Otal Ya Danne Masu Dibar Ganima a Jihar Kano, An Rasa Rai

Ginin Daula Otal Ya Danne Masu Dibar Ganima a Jihar Kano, An Rasa Rai

  • Ginin Daula Hotel da gwamnatin Kano ta fara rusawa ya karisa ruftawa kan masu ɗibar ganima, mutum ɗaya ya riga mu gidan gaskiya
  • Hukumar kwana-kwana ta ce jami'anta sun ceto mutum uku zuwa yanzu amma har yanzu an ce da sauran mutane a ciki
  • Wasu da abun ya faru a kan idonsu sun ce ɓarayin kayan na kokarin sace rodikan ƙarfe, ba zato ginin ya danne su da karfe 2:30 na rana

Kano - Wasu mutane da ake tsammanin masu ɗibar ganima ne da ke sace kayan gini sun maƙale a ɓaraguzan ginin Daula Hotel da aka rushe a jihar Kano.

Ginin na ɗaya daga cikin kadarorin gwamnati da aka rushe bisa umarnin gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya lashi takobin kwato kadarorin da ya ce an cefatar ba kan ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

Wani Ɗan Kasuwa Ya Maka Matarsa a Kotu, Ya Nemi a Raba Aurensu Saboda Ta Kara Aure Kan Aure

Ginin Daula Otal ya rufta kan mutane.
Ginin Daula Otal Ya Danne Masu Dibar Ganima a Jihar Kano, An Rasa Rai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa ɗaya daga cikin mutanen da ginin ya danne ya riga mu gidan gaskiya, wasu uku kuma sun ji munanan raunuka, amma har yanzun ba'a ciro wasu ba.

Ganau sun bayyana cewa lamarin ya auku da misalin ƙarfe 2:30 na rana yayin da ɓarayin ke kokarin zare rodika daga cikin tarkacen ginin da aka rusa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kwana-kwana a jihar Kano, Saminu Yusif, wanda ya je wurin, ya bayyana cewa zuwa yanzu tawagarsa ta zaƙulo mutum uku daga cikin ginin.

A kalamansa, Yusuf ya ce:

"Jami'an mu sun ceto mutum uku, ɗaya ya karye a ƙafa amma 'yan uwansa sun ɗauke shi, ragowar biyun kuma suna nan an barsu bayan ciro su daga cikin tarkacen ginin."
"An gaya mun har yanzu akwai sauran mutane a ciki, amma daga nan zuwa lokacin da zamu samu nasarar zaƙulo su, ba zamu iya faɗin adadinsu ba. Amma kamar yadda kuke gani jami'ai na kan aiki."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Abdulsalam Abubakar a Villa, Bayanai Sun Fito

Yadda ginin ya ruftawa barayin kayan

Channels tv ta ruwaito wani ganau, Isah Ibrahim, na cewa:

"Muna kan bene muna aiki kuma mafi yawan waɗannan da ake ce wa masu ɗibar ganima suna ƙasa suna ɗauki ɗai-ɗai. Inda aka samu matsalar shi ne wasu na sama, su kuma na ƙasa ke rage ƙarfin ginin."

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Bukatar Abba Gida-Gida

A wani rahoton na daban Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida.

A wata wasiƙa da ya tura majalisar, gwamnan ya nemi ta amince ya naɗa masu ba da shawara 20da zasu taimaka masa wajen sauke haƙƙin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: