Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Ci Gaba Da Aikin Rusau Duk Da Sukar Da Take Sha
- Gwamnatin jihar Kano ta dawo da aikin rusa gine-finen da gwamnatin baya ta siyar duk da adawar da tsohon gwamna Ganduje ya nuna da hakan
- An rusa shagunan da ke kusa da filin wasa na Sani Abacha, GSS Kofar Nasarawa, da gine-ginen kusa da GGSS Dukawiya
- Duk da sukar lamarin, gwamnati ta jajircewa don ci gaba da aikin rusau yayin da shaidu suka tabbatar da ruguza wani bangare na makarantar yan mata a Dukawiya
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta koma bakin aikin da ta faro na rusa gine-ginen da aka yi a wuraren gwamnati da ake zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje da siyar da su, rahoton Daily Trust.
Hakan na zuwa ne yan kwanaki kadan bayan tsoffin gwamnonin jihar, Rabiu Musa Kwankwaso da Ganduje sun yi musayar yawu kan rushe-rushen da ake yi a jihar.
Yanzu-Yanzu: "Zan Iya Marin Kwankwaso Da Mun Hadu a Villa" Ganduje Ya Fusata da Abinda Ke Faruwa a Kano
Yan siyasar biyu sun ziyarci shugaban kasa Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, kuma an dauko batun rusau din ake yi.
Rusau a Kano: Abun da tsohon gwamna Ganduje ya ce
Yayin da Ganduje ya ce ya fada ma shugaban kasar cewa rushe-rushen baya bisa ka'ida kuma yana da hatsari ga jihar, Kwankwaso ya yi ikirarin cewa ya fada ma shugaban kasar cewa tsohon gwamnan ya siyar da muhimman wurare ciki harda masallatai da makabarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, an ci gaba da aikin rusau a safiyar ranar Lahadi, kuma an tattaro cewa gine-ginen da aka rusa sun hada da shaguna da aka gina jikin bangon filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, GSS Kofar Nasarawa da ke fuskantar hanyar IBB da kuma gine-ginen GGSS Dukawa, Goron Dutse.
Abun da ganau suka ce game da rusau a Kano
Ganau sun ce hukumar Tsare-Tsare da Raya Birane ta Kano (KNUPDA) karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rusa wani bangare na makarantar Sakandaren gwamnati ta yan mata da ke Dukawiya a cikin garin jihar.
Duk da sukar da ya biyo bayan shirin, mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da rusa gine-ginen.
Ina iya marin Kwankwaso da ace mun hadu a Villa, Ganduje
A wani labarin, mun ji a baya cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa idan da ya hadu da magajinsa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, a fadar shugaban kasa da ke Abuja da ya mare shi.
Kwankwaso dai ya gana da shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng