“Gwamnan Na Cikin Koshin Lafiya”: Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Motocin Yahaya Bello
2 - tsawon mintuna
- Mahara sun farmaki ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Asabar, 3 ga watan Yuni
- Yan daban dauke da bindigogi sun sha gaban ayarin motocin gwamnan sannan suka far masu
- Gwamnan na cikin koshin lafiya amma wasu daga cikin hadimai da masu tsaronsa sun samu rauni
Lokoja, Jihar Kogi - Wasu da ake zaton yan daba ne a ranar Asabar, 3 ga watan Yuni, sun farmaki ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, wanda ke a hanyarsa ta dawowa daga Abuja zuwa Lokoja.
Wata sanarwa da kwamishinan labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar kuma aka gabatarwa manema labarai, ya bayyana cewa wasu mutane da ake tunanin magoya bayan Alh Muritala Yakubu Ajaka ne sun tare ayarin gwamnan sannan suka farmake su.
Yadda al'amarin ya faru
Ya ce sun kai harin ne da misalin karfe 12:30 na ranar Asabar, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Premium Times ta nakalto yana cewa:
"Harin ya faru ne a kusa da sansanin sojin ruwa, yan kilomita kadan daga Lokoja inda ayarin motocin Muritala Yakubu Ajaka suka toshe hanya bayan sun hango na gwamnan sannan wasu yan barandarsa suka fara harbi kan mai uwa da wahabi kan ayarin gwamnan.
"Wata motar Tundra dauke da logon SDP da tutar SDP ta kuma tsare gaban motar gwamnan kuma wadanda ke cikin motar na SDP din sun kasance yan daba dauke da bindigogi. Gwamnan ya bar wajen ba tare da wata matsala ba kuma babu wani abun fargaba domin Gwamnan na cikin koshin lafiya.
"Wasu masu tsaro da sauran hadiman gwamnan sun ji raunuka daban-daban kuma an kwashe su zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.'
"Muna umurtan mutanen jihar Kogi da su ci gaba da kwantar da hankalinsu domin jami'an tsaro na kan lamarin don ganin sun kama yan daban da suka kai harin. Gwamnatin jihar za ta tabbatar da ganin cewa an dauki mataki don dai za a gurfanar da maharan.
"Gwamnan ya yi gargadin cewa kada wani dan APC da ya kai harin ramuwar gayyana domin rashin tsaro daga kowani bangare zai gamu da fushi mai tsanani."
Asali: Legit.ng
Tags: