EFCC Ta Titsiye Tsohon Gwamnan APC da Ya Sauka Kan Wawure N4bn
- Jami'an hukuma EFCC sun tsare tsohon gwamnan jihar Ekiti da tambayoyi kan zargin wawure kuɗi biliyan N4bn
- Rahoto ya nuna tsohon gwamnan na APC, Kayode Fayemi, ya isa ofishin EFCC na Ilorin, jihar Kwara da karfe 9:40 na safiyar Alhamis
- Tun a watan Mayu EFCC ta gayyaci Fayemi amma ya nemi a ɗaga masa ƙasa zuwa bayan ya gabatar da littafinsa
Kwara - Rahoton Punch ya nuna cewa yanzu haka tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, yana Ofishin hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) reshen jihar Kwara.
Jami'an hukumar EFCC sun titsiye tsohon gwamnan na jam'iyyar APC bisa zargin halasta kuɗin haram kimanin naira biliyan N4bn.
Wata majiya mai ƙwari ta shaida wa wakilin jaridar cewa Dakta Fayemi ya isa Ofishin EFCC da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara da misalin 9:40 na safiyar Alhamis.
Idan baku manta ba a watan Mayu, Fayemi ta hannun lauyansa, Adeola Omotunde, SAN, ya roki EFCC ta jinkirta masa ya gabatar da littafin girmamawa ga shugaban ƙasa Buhari ranar 19 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bayan gabatar da wannan littafi da ya rubuta, zai amsa gayyatar da hukumar ta masa domin amsa tambayoyi kan zargin halastawa kansa kuɗin haram.
A rahoton Daily Trust, wata majita ta tabbatar da cewa:
"Fayemi ya isa ofishin EFCC na jihar Kwara da misalin ƙarfe 9:40 na safe, yanzu haka jami'anmu sun tasa shi gaba da tambayoyi kan tuhumar karkatar da biliyan N4bn."
"Bani da tabbacin ko zasu sake shi yau ko kuma zasu tsare shi, amma abinda nake son ku sani ba shi kaɗai ne tsohon gwamna da yanzu haka EFCC ke tuhuma ba."
Yayin da aka tuntuɓe shi, kakakin EFCC na ƙasa, Wilson Uwujaren, ya tabbatar cewa Fayemi na hannun jami'ai amma yaƙi yarda ya yi ƙarin bayani.
"Eh, dagaske ne yana tare da mu, yana ofishinmu na Ilorin don amsa tambayoyi amma daga haka ba zan iya ƙara cewa komai ba," inji shi.
Zanga-Zanga Ta Barke a Jihar Edo Kan Tashin Farashin Man Fetur
A wani rahoton na daban kuma Mutane sun fito kan tituna zanga-zanga biyo bayan tashin farashin litar man Fetur wanda a yanzu ya haura N500.
Shugaban tawagar masu zanga-zangar ya ce sun fito kan Tituna ne domin jawo hankalin shugaban ƙasa, Tinubu, ya ɗauki matakin soke ƙarin da aka samu kan kowace lita.
Asali: Legit.ng