Ba Mu Shirya Zanga-Zanga Kan Cire Tallafin Man Fetur Ba Zuwa Yanzu – Kungiyar Kwadago

Ba Mu Shirya Zanga-Zanga Kan Cire Tallafin Man Fetur Ba Zuwa Yanzu – Kungiyar Kwadago

  • Kungiyar NLC ta yi watsi ta yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa tana shirin gudanar da zanga-zanga kan cire tallafin man fetur
  • Kungiyar kwadagon ta ce bata shirya kowace zanga-zanga ta gama gari a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni ba
  • Ta ce za ta dai yi wani zama don tattauna batun karin kudin man fetur din kuma za ta sanar da matakin da ta dauka bayan taron

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana cewa bata shirin gudanar da kowace zanga-zanga na gama gari a ranar Juma'a kan tashin gauron zabi da farashin man fetur ya yi sakamakon cire tallafin mai.

Kungiyar ta ce koda dai ta fusata da abun da ta bayyana a matsayin "karin farashi na rashin hankali da aka yi don jefa talakan Najeriya cikin wahala" babu zanga-zanga kan haka tukuna, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Yan Siyasa Da Tinubu Zai Iya Nadawa a Matsayin Ministoci Ya Bayyana

Shugaban kungiyar kwadago da Shugaban kasa Bola Tinubu
Ba Mu Shirya Zanga-Zanga Kan Cire Tallafin Man Fetur Ba Zuwa Yanzu – Kungiyar Kwadago Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni dauke da sa hannun shugaban sashin labarai na NLC, Benson Upah, shugaban kungiyar, Kwamrad Joe Ajaero, ya yi martani ga rahotannin da wasu ke yadawa cewa sun shirya zanga-zanga a ranar Juma'a.

Da yake bayyana matsayin kungiyar, Ajaero ya yi bayanin cewa kungiyar za ta gudanar da wani taro a ranar Juma'a domin tattauna batun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar The Nation ta nakalto yana cewa:

"An ja hankalinmu zuwa ga wasu labarai da ke yawo a soshiyal midiya suna ikirarin cewa kungiyar kwadago ta Najeriya za ta fara zanga-zanga a gobe (Juma'a, 2 ga watan Yuni) kan karin farashin man fetur.
"Duk yadda muka kai ga fusata da wannan karin farashi na rashin hankali wanda ke nufin jefa talakan Najeriya a mawuyacin hali, ba ma shirin fara kowani zanga-zanga a gobe.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

"Abun da muke yi a yanzu shine shirya taro a gobe, Juma'a, 2 ga watan Yunin 2023 don tattauna lamarin farashin. Mun yi alkawarin sanar da yan Najeriya mataki na gaba da za mu dauka bayan taronmu.
"A kan haka, muna shawartan jama'a da su yi watsi da wadannan labaran. Ba daga kungiyar suka fito ba."

An tashi baran-baran a ganawar gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago

Mun kawo a baya cewa an tashi baran-baran a ganawar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago a ranar Laraba.

A ranar Laraba, 31 ga watan Mayu ne wakilan gwamnatin tarayya da kungiyar kwadagon suka sa labule kan cire tallafin man fetur a fadar shugaban kasa, Abuja amma ba su cimma matsaya guda ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags:
NLC