Nasir El-Rufa'i: An Haifa Wa Gwamnan APC Dan Shekara 63 Ya Mace, Hotuna Sun Fito
- Matar gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ta haifa masa santaleliyar budurwa, wacce itace ta huɗu da su ka haifa a tare da ita
- Hotunan El-Rufai da matarsa Aisha Ummi Garba El-Rufai da kuma jaririyar sun karaɗe Intanet biyo bayan ɗora su da babban ɗansa ya yi a ranar Laraba, 10 watan Mayu
- Babban ɗan El-Rufai, wato Bello El-Rufai ya nuna godiya ga Ubangiji sannan kuma ya bayyana sunan jaririyar da Fatima Layan
Matar Nasiru El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Aisha Ummi Garba El-Rufai ta haifo musu santaleliyar 'ya mace, wacce ita ce ɗiya ta huɗu da su ka haifa da gwamnan.
Daily Trust ta ce an raɗawa jaririyar suna Fatima Layan El-Rufai kamar dai yadda babban ɗan El-Rufai wato Bello El-Rufai ya sanar.

Source: UGC
A ranar Laraba, 10 ga watan Mayu ne dai Bello El-Rufai ya bayyana labarin gami da ɗora hotunan a soshiyal midiya kamar yadda PM News ma ta wallafa.
Kamar dai yadda ya rubuta a shafinsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Tare da tsatson El-Rufai na baya-bayan nan, muna farin ciki da samun ki antin mu.”
El-Rufai ya magantu kan muƙamin ministan Abuja ƙarƙashin Tinubu
Gwamnan na jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa ba ya muradin riƙe kujerar ministan birnin tarayya ƙarƙashin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.
El-Rufai, wanda yanzu haka dai ya ke da shekaru 63 a duniya, ya taɓa riƙe muƙamin ministan birnin tarayya a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, daga 13 ga watan Yuli na shekarar 2003, zuwa 27 ga watan Yuli na shekara ta 2007.
El-Rufai ya sha yabo sannan kuma ya yi suna sosai a wannan muƙami da ya riƙe na ministan birnin tarayya wanda a lokacin ya yi aiki tuƙuru wajen zamanantar da birnin na tarayya.
Da gaske ne Tinubu zai baiwa El-Rufai shugaban ma'aikata? El-Rufai ya yi bayani

Kara karanta wannan
Kafin Ya Shilla Turai, Tinubu Ya Yi Kus-Kus Da Zabin APC a Shugabancin Majalisar Wakilai, Bayanai Sun Bayyana
Nasiru El-Rufai ya musanta jita-jitar da ke yawo kan cewar ya na kuma neman muƙamin shugaban ma'aikata a gwamnatin Tinubu.
Ya ce ba wai dole sai mutum ya na cikin gwamnati ba ne zai iya bayar da gudummawarsa wajen kawo ci gaba. El-Rufai ya ƙara jaddada irin jajircewarsa wajen ganin nasarar gwamnatin Tinubu.
El-Rufai ya kuma bayyana cewa ya na da buƙatar ya ɗan huta bayan kammala wa'adinsa na gwamna, duk da dai ya ce a shirye ya ke ya riƙa bada shawarwari wajen ci gaban ƙasar.
Asali: Legit.ng
