“Bana Bukatar Saurayi”: Inji Matashiyar Budurwa, Ta Fallasa Hirarsu Da Yayanta
- Wata kyakkyawa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce bayan ta fallasa wasu daga ciki hirarrakinta da yayanta
- Ta jinjina yadda yayanta yake ji da ita, yayin da ta ce bata bukatar saurayi tun da har tana da shi
- Masu amfani da soshiyal midiya sun bayyana ra'ayinsu a kan hirar Whatsapp din yayin da suka magantu kan yadda yayansu maza ke yi da su
Wata matashiya yar Najeriya ta jinjinawa yayanta a TikTok yayin da ta wallafa sakonninsu na WhatsApp.
Sakonnin da ta wallafa ya nuna akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninta da mutumin.
A daya daga cikin hotunan hirarrakin, yayanta ya ce N100k nata ne, sannan iyayensu su rarraba N50k kowannensu.
A wani hirar kuma, ya bata N150k na kashewarta da sauran abubuwan bukata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An gano matashin yana shawartanta da ta guji yawon dare a wata hirar tasu.
Matashiyar ta jinjina masa sannan ta ce bata bukatar wani saurayi. Wallafar tata ya haddasa cece-kuce tsakanin jama'a a soshiyal midiya.
Kalli hirar tasu a nan.
Jama'a sun yi martani
being.scholastica ta ce:
"Yayana yana tare da Allah na yi kewar bawan Allan nan sososai."
dharmee ya ce:
"Irin wannan yanayin ne ke sa ni jin cewa ina ma ba ni ne dan fari ba."
Joy Ajayi ta ce:
"Ina rokon Allah ya albarkaci yayana. Don yana da zuciyar zinare."
Mhiz Awelexzy ta ce:
"Ina ma ace ina da babban yaya kamar wannan wannan ne dalilin da yasa kasancewata yar fari ke yi mun ciwo wasu lokutan."
Mara ta ce:
"Nawa sai dai ya ta kula da duk wani motsina."
Lau ra ta ce:
"Nawa yayan sai dai ya yi ta ware idanu yana neman abinci."
Budurwa mai tallan gwanjo ta siya motar miliyoyi
A wani labari na daban, wata kyakkyawar budurwa ta garzaya shafin soshiyal midiya don sanar da duniya yadda sana'ar siyar da gwanjo ya yi mata rana, har ya kai ga tana cikakkiyar yanci a matsayinta na 'ya mace.
Matashiyar dai ta ce ta mallaki mota har na miliyan 36 wanda ta siya da kudin gwanjo sannan ta bayyana cewa tana biyan naira miliyan tara duk shekara na hayar gidan da take ciki a yankin Lekki.
Asali: Legit.ng