“Yana Da Matukar Hatsari”: Likita Ya Yi Gargadi Kan Amfani Da Tukwanan Zamani na ‘Non-stick’, Bidiyon Ya Yadu
- Dakta Chinonso Egemba, wanda aka fi sani da Aproko Doctor, ya shawarci mutane kan amfani da tukunyar 'non-stick' wajen girki
- A cewar fitaccen likitan ma soshiyal midiya, tukwanan 'non-stick' masu bararren ciki na da hatsari ga kiwon lafiya
- Ya ce irin wadannan tukwanan kamata ya yi a jefar da su domin suna da tsari ga garkuwan jiki koma su kawo cutar kansa
Likitan Najeriya, Chinonso Egemba ya gargadi mutane a kan amfani da tukwanan 'non-stick' da cikinsu suka babbare.
A cewar likitan, an lullube tukwanan 'non-stick' da sinadaran Polyfluoroalkyl substances (PFAS), wadanda bai kamata ace sun bare ba.
Da zaran sun fara barewa, likitan ya ce, hakan na nufin ba mai kyau bane, kuma sinadaran PFAS na iya haifar da cuta.
Likitan Najeriya ya nunawa mutane irin tukunyar 'non-stick' da za su yi amfani da shi
Labari Mai Dadi Ga Mazauna Lagas Yayin da Sanwo-Olu Ya Sanar Da Isowar Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki, Ya Saki Hotuna
Aproko doctor ya ce PFAS da ke barwa daga kasan tukunya na nuna cewa na bogi ne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce ya kamata wadanda ke amfani da irin tukwanan da suka bare ko goge daga kasa su jefar da su tunda sinadaran PFAS na iya gurbata abinci.
Hatsarurrukan da ya ambata sun hada da cewar sinadarin na iya gurbata garkuwan jiki da kuma haddasa Kansa da rashin haihuwa.
A halin da ake ciki, wasu martani sun biyo bayan bidiyon da Aproko ya wallafa a Instagram.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@mykitchengardenn ta ce:
"Mutane ba su fahimci wannan ba. Wannan ne dalilin da yasa na fi son tukunyar karfe, sun fi karko. Mun gode da wannan, likita."
@beka.nenzar ya ce:
"Yallabai...ka fara bayanin dalilin da yasa kake da tukwanan nan har guda biyu a kicin dinka."
@stainless_beauticity ta yi martani:
"Kawai mutum ya siya tukunyar karfe ya huta. Ba dole sai kowa ya yi amfani da tukunyar 'non-stick' ba."
@chinny_005 ta ce:
"Matsalar shine cewa mutane na amfani da cokalayen miya na karfe wajen girki a tukunyar 'non-stick'. wannan ne dalilin da yasa yake babbarewa."
A wani labari na daban, jama'a sun cika da mamaki a soshiyal midiya bayan cin karo da bidiyon wani mai lalurar tabin hankali wanda ke tafiyar kilomita mai tsawo don isa jami'ar Benin.
Asali: Legit.ng