"Yana Iya Zautar Da Mutum": Yadda Matar Aure Ta Ci Amanar Mijinta Na Sunnah, Sam Ba Ta Yi Da Na Sani Ba
- Wani mutum ya bayyana yadda ya kama matarsa tana cin amanarsa wanda hakan yasa ya nemi a raba aurensu
- Mijin ya ce matar ta dade tana nuna rashin gaskiya har sai lokacin da ya gano ta
- Bayan ya tunkareta da batun wanda bata karyata ba, sannan kai tsaye ta amsa inda mutumin ya nemi rabuwa kuma auren ya mutu
Wata babbar kotu ta amince da bukatar wani magidanci da ya nemi a raba aurensa da matarsa.
Mijin ya bayyana cewar tana nuna rashin gaskiya a zamansu wanda shine ya yi sanadiyar mutuwar aurensu, jaridar Tribune ta rahoto.
Hatta ga lokacin da yake gwagwarmaya da lafiyarsa, matar bata nuna kulawa ba wanda hakan ke nuna ta daina damuwa da mijin nata tun da dadewa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mutumin ya ce:
"Na taba kama Zainab ta boye a kicin tana magana da wani mutum a kan waya. Da na nemi sanin wanene take magana da shi, sai ta zazzage ni sannan ta ci zarafina."
Mutumin ya yarda cewar babu wani abu da ke shiga tsakaninsu a bangaren auratayya, don haka ya ga akwai bukatar su rabu.
"Magabatana sun gayyaci Zainab don magance rigimar da ke tsakaninmu, amma ta ki amsa gayyatarsu. Babu sauran soyayya da zaman lafiya a gidanmu. Ina so a raba aurenmu."
Jama'a sun yi martani
Kola Olawuni ya yi martani:
"Yana iya zautar da mutum idan wani da kake so ka yarda da shi ya hukunta ka."
Jimoh Taofeek ya yi martani:
"Kallon rabuwr ma'aurata yana karw=ewa ne kan yara ya kamata mu zamo masu sauraron juna."
Adeshina Olajuwon ya ce:
"Dan uwa kai sabon shiga ne....ka sauya mahaukaciya sannan ka nemo mace mai tsoron Allah."
“Mutuwar Aure 1, ‘Da 1, Yajin Aiki 2”: Matashiya Ta Bayyana Gwagwarmayar Da Ta Sha Kafin Gama Digiri
Budurwa ta bayyana yadda ta sha fama yayin da take karatu a jami'a
A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha yayin da take karatunta na jami'a lamarin da ya kai ga har sai da suka rabu da mijinta.
Matashiyar ta ce bayan mutuwar aurenta ta yi fama da rainon dan da ta haifa a lokacin da kuma tafiya yajin aiki da suka yi har sau biyu.
Asali: Legit.ng