“Ina Zuwa Aji Duk Kwanan Duniya”: Bidiyon Mahaukaci Da Aka Gani Yana Rubutu a UNIBEN Ya Yadu
- Wani matashi dan Najeriya wanda ke da lalurar tabin hankali ya yadu a TikTok saboda soyayyarsa ga karatu
- A cikin wani bidiyo, wata matashiya da ta gano mutumin a jami'ar Benin ta yi hira da shi
- Mutumin ya tabbatar da cewar yana tafiyar kilomita masu yawa zuwa UNIBEN duk kwanan duniya, inda yake daukar darasi a tunaninsa
An gano wani mutumi mai lalurar tabin hankali wanda ke matukar son karatun boko a jami'ar Benin (UNIBEN).
A wani bidiyon TikTok da @collinaclarkefineart ya wallafa, ya ce mutumin ya ce yana tafiya mai nisa don zuwa UNIBEN a kullun kwanan duniya.
An gano mahaukaci a UNIBEN yana magana cikin hikima
Ya nanata a bidiyon cewa dole ya dunga zuwa makaranta a kullun don ya samu damar daukar darusa.
“Mutuwar Aure 1, ‘Da 1, Yajin Aiki 2”: Matashiya Ta Bayyana Gwagwarmayar Da Ta Sha Kafin Gama Digiri
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma magana ta gaskiya shi ba dalibi mai rijista bane a makarantar, domin dai darusan da yake magana a kai kawai a tunaninsa suke zuwa.
Yana da biro da takarda kuma an gano shi yana rubutu yayin da yake zaune a waje guda na makarantar.
Da budurwar wacce ta gansa ta yi hira da shi, yana ta magana cike da hikima. Matashiyar ta siya masa abinci da lemu.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@boysdem1 ya ce:
"Allah ya albarkace ki matar nan."
@Kitten ta ce:
"Magana ta gaskiya ban ji dadi ba a nan da ni."
@pretty presh12 ta yi martani:
"Ina tsananin godiya a gareki."
@user76761706067047 ya ce:
"Allah ya albarkace ki, ke din uwa ce. Ina rokon Allah ya ci gaba da yi maki albarka a harkokinki."
@thattiktokmumfromuk ta ce:
"Ba mahaukaci bane kawai dai yana bukatar taimako ne."
@user53435340322127 ya ce:
"Wannan ne dalilin da yasa ya zama wajibi yara su tsaya a makaranta saboda mutumin nan ya san ilimi na da matukar muhimmanci."
Na sha gwagwarmaya kafin kammala jami'a, matashiya ta magantu
A wani labari na daban, wata matashiyar mata da ta gama jami'a ta bayyana gwagwarmayar da ta sha tsawon lokacin da ta shafe tana karatun digiri.
Matar ta ce a tsakankanin lokacin aurenta ya mutu, ga 'da da take kula da shi kuma sun yi yajin aiki sau biyu da sauransu.
Asali: Legit.ng