Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyan Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyan Litinin a Matsayin Ranar Hutu

  • Gwamnatin Najeriya ta ba ma’aikatan Najeriya hutun rana daya don bikin murnan ranar ma’aikata da za a ranar 1 ga watan Mayu
  • Gwamnatin ta kuma yabawa ma’aikata bisa aiki don ciyar da kasar gaba ta hanyoyi daban-daban, kamar yadda ministan harkokin cikin gida ya bayyana
  • An kuma yabawa sojoji da sauran jami’an tsaro bisa aiki tukuru wajen yakar ‘yan ta’adda da masu tada kayar baya

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta ba da hutun ranar Litinin 1 ga watan Mayu a matsayin murnar ranar ma’aikata

Wannan na fitowa ne daga bakin ministan cikin gida, Rauf Aregbesola a cikin wata sanarwar da ya fitar a madadin gwamnatin tarayya.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola
Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyan Litinin a Matsayin Ranar Hutu Hoto: RAUF AREGBESOLA
Asali: Facebook

A sanarwar da sakataren dindindin na hukumar, Shuaib Belgore ya fitar a ranar Juma’a 28 ga watan Afrilu ya bayyana dalilin ba da wannan hutun.

Kara karanta wannan

Namijin duniya: Lakcara mai mata hudu ya girgiza intanet, hotunansa da, matasa da 'ya'yan sun ba da sha'awa

A cewarsa, an ba da hutun ne don yaba kokari, jajircewa da sadaukarwar ma’aikatan gwamnati a shekarar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnati na sane da kokarinku

Ya kuma bayyana cewa, gwamnati tana sane da cewa, su ne kashin bayan ci gaba da kuma ayyukan ciyar da Najeriya gaba.

A cewarsa:

“Akwai mutunci a aiki, muna bukatar sadaukarwa da sa kai domin yin aiki saboda shi ne kashin bayan ci gaban kasar.”

Ya bukaci ma’aikata da su ci gaba da rungumar dabi’ar kokari, inda yace:

“Karshen aiki shine habaka. Ta hanyar habaka ake samun wadata a fannin kayayyaki da kuma ayyukan samar da dukiya.
“Don haka, shi ne hanyar ci gaban kasa da na ma’aikaci.”

Ku ci gaba da aiki tukuru

Ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da su ci gaba da ji da kansu a matsayin ma’aikata, inda yace gwamnatin Buhari a shirye take wajen habaka jin dadinsu.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi ya gamu da fushin alkali bayan watsawa budurwarsa 'acid'

Daga karshe, ya yabawa hukumomin tsaro bisa yaki da ‘yan ta’adda da masu tada kayar baya a yankuna daban-daban na kasar.

Gwamnatin Najeriya na ci gaba da kawo hanyoyin saukaka aiki ga ma’aikatan kasar don habaka rayuwarsu.

An fara biyan ma’aikata karin 40% na albashi

A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta bayyana karin 40% cikin albashin wasu daga cikin ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Wannan na zuwa ne a yunkurin gwamnati na cire tallafin man fetur da ke tafe nan ba da jimawa ba.

Rahoto ya bayyana adadin kudaden da aka fara biyan ma’aikatan da ke tsammanin gyara a kowane lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.