“Menene Amfanin Haka?” Hoton Gidan Laka Da Aka Sa Wutar Solar Da DSTV Ya Yadu

“Menene Amfanin Haka?” Hoton Gidan Laka Da Aka Sa Wutar Solar Da DSTV Ya Yadu

  • An wallafa hoton gidan laka da ya yadu a soshiyal midiya kuma tuni ya ja hankalin jama'a sosai
  • Hoton ya nuno wani tsohon gidan lakan a wani kauye inda mamallakinsa ya kawata abunsa da kayan alatu na zamani
  • Gidan na dauke da na'urar hasken rana guda biyu a saman rufi da kuma DSTC wanda aka daura a saman pal waya

Hoton wani gidan jan laka da aka kawata da kayan alatu a wani kauye a Najeriya ya bayyana a dandalin soshiyal midiya.

Hoton ya hasko wani gidan laka da aka kawata da na'urar kallo na DSTV makale a saman pal waya kusa da gidan.

Matashi da gidan laka mai dauke da solar
“Menene Amfanin Haka?” Hoton Gidan Laka Da Aka Sa Wutar Solar Da DSTV Ya Yadu Hoto: Dexterouz11
Asali: Getty Images

Har ila yau, an hango na'urar lantarki mai amfani da hasken rana wanda aka sanya a saman rufin gidan.

Dexterouz11, wanda ya wallafa hoton a manhajar Twitter ya ce:

Kara karanta wannan

Jirgin saman NigeriaAir Zai Fara Tashi Kafin Shugaba Buhari Ya Bar Aso Rock – Minista

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kawata ta ga wannan a kauyenta. Gidan laka dauke da DStv da wutan solar a saman rufi. Menene dalilin da yasa mamallakin wajen ke jin dadin zama a gidan laka? Menene amfanin wannna."

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@OyekachukwuN ya ce:

"Kwanciyar hankali da nutsuwa shine komai."

@dexterouz11 ya amsa da:

"Hafa fa ko."

Matashi ya gina hadadden gidan laka da naira miliyan 1.3

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wani dan gajeren bidiyo da ke nuna sabon gidan laka da aka gina ya samu mutum fiye da 720k da suka kalle shi a TikTok.

Wani mai suna Lawrance, wanda ya shahara a harkar gine-gine shine ya wallafa bidiyon a ranar 18 ga watan Oktoba.

Bidiyon wanda ya shafe tsawon sakan 39 ya nuna yadda aka gina gidan tun daga farko har karshe. Abun da ya fi jan hankali game da bidiyon shine cewa Lawrance bai yi amfani da bulo ba wajen ginin. Maimakon haka, ja laka da katakai ya yi amfani da shi sannan daga baya ya yi shafe da siminti.

Masu amfani da TikTok da suka nuna sha'awarsu na son mallaka irin gidan sun tambayi abun da aka kashe a kansa, kuma Lawrance ya ce gaba daya naira miliyan 1.3 (Ksh386,000) aka kashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel