“Suna Jin Dadi”: Matashi Ya Girkawa Karnukansa Taliya Dauke Da Kaza Da Kifi
- Bidiyon wani mutumi yana ciyar da karnukansa taliya da nama ya haddasa cece-kuce a tsakanin mutane da dama a soshiyal midiya
- Mutumin ya dauki lokaci wajen girkataliyan yayin da ya zuba ruwan zafi a babban tukunya sannan ya basu suka ci
- Masu amfani da TikTok da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa karnukan sun ma fi mutane da dama samun abinci mai kyau
Wani matashi dan Najeriya, @drme69, ya wallafa Wani bidiyo da ke nuna lokacin da yake dafawa karnukansa taliya a wani katon tukunya.
A farkon bidiyon, mutumin ya zuba taliyar a wani katon bakin tukunya. Batak nan, sai ya zuba tafasasshen ruwa sannan ya bar shi ya dahu. Ya zuba sinadarai da maza da kifi.
Matashi ya ciyar da karnukansa taliya, kaza da kifi
Bayan ya gauraya abincin a wuri daya, mutane da dama sun ce da gani zai yi dadi. Matashin ya zuba abincin a kwanuka daban-daban sannan ya kai kejinan karnukan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ciyar da kananan karnukansa alkama kawai. Mutane da dama sun bayyana cewa karnukan sun ma fi su cin abinci mai lafiya.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun tofa nasu
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tattara martani fiye da 1200 da ‘likes’ fiye da 59,000.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:
Chi baby ta yi mamaki:
“Me yasa abincin karnuka ya shiga raina?”
Austinecruise On IG ya ce:
“Alhalin mutane na shan garin kwaki!”
doraxo__ ya ce:
“Wadannan karnukan sun fi wasu mutane jin dadi.”
Prisca Omah ta ce:
“Awwww karamin ciki abincinsa daban.”
book ya ce:
“Dan autan karen na jin dadi faaa cocoa pops ko Menene wannan.”
Zakara ya yi sanadiyar maka wani mutum a kotun Kano, an bukaci an yanka shi
A wani labarin, wasu mazauna jihar Kano sun yi karar wani makwabcinsa a gaban wata kotun majistare da ke zama a Gidan Murtana saboda zakaransa da ya hana masu sakat a unguwa.
Masu karar sun zargi zakaran mutumin da yawan cara tare da hana su yin bacci cikin dadi saboda kiriniyarsa. Mai Shari'a a kotun ta yi umurnin yanka shi.
Asali: Legit.ng