Iyali Sun Yi Amfani Da Tukunya Maimakon Akwatin Gawa Yayin Bikin Mutuwar Kakarsu
- Wasu iyali da suka yi bikin mutuwar kakarsu cikin salo ta hanyar amfani da akwatin gawa na musamman sun shahara a Instagram
- A bidiyon, iyalin sun yi amfani da akwatin gawa da aka kera kamar tukunya don bikin mutuwar kakar tasu
- A cewar masu amfani da soshiyal midiya, hakan ya nuna kakar tasu gwanar iya girki ce wacce ta ciyar da yaranta da kyau
Wani bidiyo da ya yadu a Instagram ya nuno lokacin da wasu iyali suka kirkiri sabon salo don bikin mutuwar kakarsu wacce ta kwanta dama.
Iyalin sun yanke shawarar kera akwatin gawa mai kama da tukunya don nunawa kakar tasu yadda suke tsananin son girkinta a lokacin da take raye.
An kuma hasko yadda aka dauki akwatin gawar mai siffar tukunya ana zagayawa da shi yayin da iyalin ke bikin mutuwar kakar tasu.
Mutane da dama sun yarda cewar akwatin gawar ya kasance a saukake kuma na musamman, sai dai hakan bai yi wa wasu masu amfani da soshiyal midiya da suka yi martani ga bidiyon ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyon sun yi tunanin wani salo ne da bai tafi daidai ba kuma suna ganin da ma ba a yi tunaninsa ba tun farko.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tara martani fiye da 3000 a Instagram.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
shoppingplaze ta yi martani:
“Ta yaya suka shigar da iya ciki?”
iambiggysteve ya ce:
“Ina da tabbacin za su kara dafaffen kwai daya ko biyu a cikin akwatin gawar. Yan Ghana basa wasa da kwai.”
micie_pee ta yi martani:
“Ina da tambayoyi da dama haka take da gajarta ko na tambayesu kun tankwasheta a ciki ne ko kun lallaya ta? Mai girki ce a baya?”
wallpaperplace ya rubuta:
“An ninke gawar ne? Ko kun lankwasa shi ne?? Ta yaya mutum zai huta lafiya a irin wuri haka.”
A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya ya cika da farin ciki bayan wani butum-butumi ya gabatar masa da abincinsa da ya yi oda a wani gidan cin abinci.
Asali: Legit.ng