NCC ta Bayyana Babban Dalilin Da Yasa Datar Mutane Ke Saurin Ƙarewa

NCC ta Bayyana Babban Dalilin Da Yasa Datar Mutane Ke Saurin Ƙarewa

  • Ƴan Najeriya na cigaba da yin korafi akan rashin sanin dalilin da yasa datar su ke saurin zuƙewa
  • Wasu masu amfani da Data sunce an ragewa datar nagarta ne
  • Yayin da wasu suke zargin kamfanonin da suke siyan data da "Sibaran-nabayyen" yar datar da suka siya

Abuja - Hukumar sadarwa ta Najeriya tace ta damu da korafe korafen da ƴan ƙasa ke cigaba da yi mata.

Korafin da ƴan Najeriya ke faman zabga mata shine akan yadda ake sukuwar sallah akan datar da suka saya ta sati, wata ko shekara.

Wannan dalili yasa hukumar sadarwar ta Najeriya, tayi fargar daji wajen gano ummul-aba-isin da yasa hakan ke faruwa.

NCC data
NCC ta Bayyana Babban Dalilin Da Yasa Datar Mutane Ke Saurin Ƙarewa Hoto: Legit.ng
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A binciken da hukumar tayi na ƙwara-ƙwatan, ta gano cewar cinyewar data a waya ko na'ura mai ƙwaƙwalwa ta samo asali ne ga yadda ake samun sababbin kayan na'urori masu shan data a duk faɗin duniya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

Hukumar sadarwar ta Najeriya ta zargi masu amfani da waya da alhaƙi shanye datar su da kansu, inda tace hakan yana da nasaba da kayan da suke siya sababbi masu amfani da data mai nauyi.

Hukumar tace, saurin sauke abubuwa zuwa kan waya da kuma saurin haɗa na'ura da yanar gizo gizo a ɗan kankanin lokaci nada nasaba da saurin cinyewar data.

Wasu daga korafin masu amfani da data ya haɗa da, korafin cewa datar da suke siya ta wata ba yi musu wata take ƙarewa.

Yayin da wasu suka ce, datar sati bata yi musu sati, kawai sai dai suji an cire su daga shiga yanar gizo gizo.

Da yake bayani ga cincirindon mutane a taro na 91 da aka yi na "Majalisar Masu Amfani da Waya mai taken "Zuƙewar Data" Mataimakin shugaban NCC na ƙasa, Farfesa Umar Garba Danbatta yace:

"Masu amfani da Data suna fuskantar zuƙewar data, kuma suna mana ƙorafi a NCC. "

Kara karanta wannan

Bankuna Sun Shiga Damuwa Saboda Mutane Basa Zuwa Ajiye Kuɗi

Ya cigaba da cewa:

"Illar da aka samu ta COVID-19 itace babbar jigo a cikin matsalar, domin ta haifar da samuwar sababbin ababen kimiyya da fasaha."

Ya ƙara da cewa:

"Hakan ne yasa aka samu sababbin hanyoyi nayin abubuwa a duniya.
"Harkar sadarwa a Najeriya itama abin ya taɓa ta, saboda an samu shigowar manya manyan na'ura masu ƙwaƙwalwa, agogo mai waya, da sauran kayan zamani masu kyau wanda yabawa masu amfani da waya damar zaɓi maras adadi".

Ya shaida wa jaridar Thisday cewar:

"Hakan yasa aka shiga amfani da fasahar wajen amfani da kafafen sadarwa na zamani, da tura saƙo na ujula."

"Ko shakka banayi, babban abinda yake sawa abubuwan nan suyi aikin su yadda yakamata shine mahaɗa (Network)."

Ya ƙarkare da:

"To nan batun zuƙewar data tazo, domin idan da mahaɗa mai kyau, za'a samu yin abu yadda ya kamata, daga nan kuma data zata zuƙe, shine mutane suke cewa ana cire musu data ba bisa ƙaida ba."

Kara karanta wannan

Riya ne: Saudiyya ta fusata, ta fadi abin da za ta yiwa masu daukar hoto a lokacin Hajji da Umrah

An Samu Wata Na'ura da Zata Hana Ma'aurata Ƙarya da Yaudara

A wani labari mai kama da wannan, jaridar legit.ng fa ruwaito yadda masu kirkira a fagen sadarwar zamani su ka hada wata na'ura da zaka iya gane matarka ta yaudareka ko mijinki ya yaudare ki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar

iiq_pixel