Allah Ya Yiwa Shahrarren Dan Kwangila a Jihar Kano, Alhaji Sani Dahiru Yakasai, Rasuwa
- Rai bakon duniya. Daya daga cikin manyan dattawa a jihar Kano ya amsa kirar ubangiji
- Rahoto ya nuna cewa dan kwagilan ya rasu ne bayan doguwar jinya da yayi fama da ita
- An yi jana'izarsa a gaban gidan sarki kuma an birneshi a Tarauni
Shahrarren dan kasuwa kuma dan kwangila a jihar, Alhaji Sani Dahiru Yakasai, ya rigamu gidan gaskiya.
Marigayin ya kasance shugaban kamfanin gine-gine na SDY Construction Company.
Ya rasu ranar Alhamis.
DailyTrust ta ruwaito wata majiya da cikin gida cewa attajirin ya rasu ne ayan daguwar jinya da yayi fama da ita.
Majiyar ta kara da cewa SDY ya rasu yana mai shekaru 68 a duniya.
Ya bar mata, 'yaya, da jikoki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An yi Sallar Jana'izarsa a fadar Sarki, Kofar Kudu da safiya Juma'a misalin karfe 8 na safe kuma an bizneshi a makabartar Tarauni.
Yan uwa da abokan arziki sun yi addu'an Allah ya jikansa da rahama.
Dan takaran kujerar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano na NNPP, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), sun kai gaisuwar ta'aziyya gidan marigayi.
Ya yi addu'an Allah ya kyautata bayansa kuma ya azurta shi da gidan Aljannah.
A jawabin da ya daura a shafinsa na Tuwita, Kwankwaso ya bayyana cewa:
"Da safiyar nan nakai gaisuwar ta'aziyyagidan iyalandan kasuwan jihar, Alhaji Sani Yakassa(SDY) wanda ya rasu ranar Alhamis."
"Allah ya bashi Aljammah kuma ya kyautata karshensa."
Kwankwaso ya yi farin ciki inda ya karbi bakuncin yan Kwankwasiyya da sukayi nasara
Da zu mun kawo muku rahoton cewa Jagoran jam'iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP kuma wanda yayi mata takarar kujerar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karbi bakuncin sabbin zababbun majalisar dokokin tarayya.
Sabbin zababbun yan majalisar guda goma sha bakwai (17) sun samu nasara ne karkashin jam'iyyar a jihar Kano.
Sun ziyarci jagoran darikar Kwankwasiyyan ne a gidansa inda suka dauki hotuna tare da takardar shaidan samun nasara da hukumar INEC ta basu.
Daga cikinsu akwai wadanda suka taba zama a majalisa irinsu Alu Madakin Gini da kuma Abdulmumini Jibrin Kofa.
Asali: Legit.ng