Hukumar INEC Ta Gwangwaje Zababbun Ƴan Majalisar Wakilai Da Satifiket Ɗin Cin Zaɓe
- Zababbun ƴan majalisar wakilan Najeriya sun karɓi shaidar cin zaɓen su a hannun hukumar zaɓe ta ƙasa INEC
- A yau ne dai aka yi bikin miƙa satifiket ɗin cin zaɓen ga zababbun ƴan majalisar wakilan ta Najeriya
- Hukumar INEC ta gabatarwa zaɓaɓɓun ƴan majalisa 325 satifiket ɗin lashe zaɓen da suka yi a mazaɓu daban-daban
Abuja- Hukumar zaɓe mai zamn kanta ta ƙasa (INEC) ta miƙa satifiket 325 na lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun ƴan majalisar wakilai a Najeriya.
Zaɓaɓɓun ƴan majalisar wakilan sune suka yi nasara a zaɓen da akayi tare da na shugaban ƙasa a ranar 25, ga watan Fabrairun 2023.
An dai miƙa musu satifiket ɗin ne a cibiyar taro ta ƙasa da ƙasa dake a birnin tarayya Abuja. Rahoton Premium Times
Jerin sunayen da hukumar ta saki a ranar Talata, ya nun har yanzu babu waɗanda suka yi nasara a cikin mazaɓu 35 a dalilin wasu wuraren za a yi zaɓen cike gurbi ko an kai ƙara kotu kan zaɓen.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jam'iyyu takwas ne kawai cikin jam'iyyu goma sha takwas suke da wakilci a cikin majalisar wakilan, a cewar shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Mahmood Yakubu.
Jam'iyyun sune, All Progressives Congress (APC), the Peoples Democratic Party (PDP), All Progressives Grand Alliance (APGA), Social Democratic Party (SDP), Labour Party (LP), New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Sauran sune African Democratic Congress (ADC) da kuma Young People Party (YPP).
Jam'iyyar APC mai mulki har yanzu otace ke riƙe da kujeru mafiya rinjaye a majalisar da kujeru 162, sannan babbar jam'iyyar adawa ta PDP mai kujeru 102. Jam'iyyun LP da NNPP suna 34 da 18 kowacen su.
2023: INEC Ta Soke Zabe a Mazabar Shugaban Masu Rinjaye, Ado Doguwa
A wani labarin na daban kuma, hukumar zaɓe ta INEC ta soke zaɓe a mazaɓar Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta Najeriya.
A baya dai har hukumar ta bayyana shugaban masu rinjayen a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Asali: Legit.ng