Mambobin Jam'iyyar NNPP Sun Fito Zanga-Zanga Kan Sakataren INEC Dake Kano
- Wasu mambobin jam'iyyar NNPP sun tafi zanga-zanga hedkwatar hukumar zabe ta INEC
- Wannan ya biyo bayan zanga-zangan da suka yi jiya Talata kan kwamishanan da suke zargin za'a turo Kano
- Yau dai saura kwanaki uku zaben gwamnonin Najeriya kuma ta jihar Kano na cikin masu zafi
Kano -Mambobin jam'iyyar adawa ta New Nigeria Peoples Party, NNPP, a jihar Kano sun fito zanga-zanga kan zargin cewa Sakataren hukumar zabe INEC na jiha ya hada kai da jam'iyyar APC.
Wannan sakatare na hukumar INEC da ake zanga-zanga a kansa sunansa Alh. Garba Lawan Muhammad.
Freedom Radio ta ruwaito cewa masu zanga-zangar na zargin Alhaji Lawan ya hada kai da jam'iyyar APC dake kan mulki don yin magudi a zaben gwamnan jihar.
An yi zanga-zanga ne gaban hedkwatar hukumar INEC dake Kano.
Zaben gwamnan jihar Kano da sauran gwamnonin Najeriya zai gudana ne ranar 11 ga Maris, 2023.
Kalli hotunan:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mambobin Jam'iyyar NNPP Sun Fito Zanga-Zanga Kan Sabon Kwamishanan Yan Sandan Da Za'a Tura Kano
Jiya mun kawo muku labarin cewa mambobin jam'iyyar adawa ta New Nigeria Peoples Party, NNPP, a jihar Kano sun fito zanga-zanga kan zargin cewa hukumar yan sanda na shirin tura wani sabon kwamishanan yan sanda Kano.
Wannan kwamishana mai suna, Balarabe Sule, da NNPP ke zanga-zanga kansa, tsohon dogarin gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ne.
Tsohon Sakataren hukumar TetFund, Baffa Bichi, ne ke jagorantar wannan zanga-zanga.
Asali: Legit.ng